Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Shugaban PDP Ya Faɗi Yada Za a Kayar da APC a Zaɓen 2027
- Umar Damagum ya bayar da tabbacin cewa jam'iyyar PDP na shirin dawowa kan turbar nasara a babban zaɓen 2027 mai zuwa
- Muƙaddashin shugaban PDP ya baiwa mambobin jam'iyyar hakuri kan rikicin cikin gida, inda ya ce za su karɓe mulki daga hannun APC
- Gwamna Makinde ya yi addu'ar Allah ya bai wa jam'iyyar PDP damar sake kafa gwamnati a Najeriya a kakar zaɓe na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa Umar Damagum, ya tabbatar wa mambobin jam'iyyar cewa PDP za ta dawo kan turbar nasara a 2027.
Damagum ya bayar da wannan tabbacin ne a Umuahia a wurin liyafa da bikin cika shekaru 76 na shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Adolphus Wabara.
Kamar yadda jaridar Punch ta kawo, Damagum ya ce jam'iyyar PDP ta gama shirye-shiryen karɓe mulkin Najeriya a babban zaɓe mai zuwa a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bisa la'akari da aiki tuƙuru da muke yi, zamu dawo kan ganiya cikin ƙoshin lafiya da nasara," in ji shi.
Daga nan kuma sai shugaban jam'iyyar ya yi kira ga ɗaukacin mambobin PDP su ƙara haƙuri, za su warware duk wata matsala tare da magance kalubalen da jam'iyyar ke fama da su.
Gwamna Mbah yabawa Wabara
Tun da farko, babban mai masaukin baki kuma gwamnan jihar Enugu, Peter Mba, ya ce Wabara “ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da jam'iyyar mu ke kan ganiyarta."
Kuma gwamnan ya bayyana fatansa cewa Sanata Wabara "zai yi amfani da gogewarsa wajen cicciɓo jam'iyyar ta dawo kan mulki."
A jawabinsa, shugaban taron kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce an shirya wannan liyafa ne domin taya murna ga mutumin da Abia ta haƙura ta bai sa PDP.
PDP na shirin karɓe mulki a 2027
A rahoton Tribune Nigeria, Gwamna Makinde ya yi addu'ar cewa a kakar siyasa ta gaba, "Allah ya ba PDP damar kafa gwamnati a Najeriya."
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, da takwaransa na Edo, Godwin Obaseki da mambobin PDP-BoT da mwamitin ayyuka na kasa sun halarci taron.
Wani mamban PDP kuma jigo, Abdullahi Kabir, ya faɗawa Legit Hausa cewa lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su natsu, su canza gwamnatin APC.
A cewarsa, abu ne mai wahala sauke gwamnati mai ci amma a yanzu kowa ya ji a jikinsa.
A kalamansa ya ce:
"Muna nan a PDP kuma tuni muka fara aiki da tsare-tsaren yadda za mu samu nasara a 2027. Farko dai abin da ya kamata, ita uwar jam'iyya ta ƙasa ta ɗinke ɓaraka.
"Duk shirin da zamu yi idan har kanmu ba haɗe yake ba, bana tunanin zamu kai labari, Tinubu mutum ne mai basira da dabarar siyasa, saboda haka dole PDP ta tashi tsaye.
Atiku ya soki mulkin Tinubu
A wani rahoton kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya magantu kan shekara guda da shugaba Bola Tinubu ya shafe a karaga.
Atiku Abubakar ya bayyana irin hanyoyi marasa ɓullewa da shugaba Bola Tinubu ya bi wajen kawo Najeriya halin da take ciki a yau.
Asali: Legit.ng