Hotuna da Bidiyo: Mata Sun Ɓarke da Zanga-Zanga a Hedkwatar APC Ta Ƙasa
- Wasu fusatattun mambobin jam'iyyar APC mata sun mamaye hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a
- Dandazon matan sun gudanar da zanga-zanga ne domin nuna rashin jin daɗinsu da halin shugabar matan APC Mary Alile-Idele
- Legit Hausa ta gano cewa matan da suka yi wannan zanga-zanga karkashin ƙungiyar mata masu kishi, sun nemi Alile Idele ta yi murabus
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wasu gungun mata da suka fito zanga-zanga sun mamaye hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Abuja ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu.
Dandazon matan sun buƙaci shugabar matan jam'iyyar APC ta ƙasa, Mary Alile-Idele ta yi murabus daga kan muƙaminta.
Suna zargin Alile-Idele da rashin kulawa da mambobi mata a APC, sannan tana amfani da kujerarta wajen cika wani burinta na ƙashin kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, zanga-zangar ta gudana ne karkashin jagorancin Rebecca Sheneni, kodinetar ƙungiyar mata masu kishin APC.
Meyasa matan APC ke zanga-zanga?
Yayin da take hira da ƴan jarida, shugabar masu zanga-zanga ta ce maimakon ta maida hankali wajen kula da matan APC, shugabar matan jam'iya ta koma tallata kasuwancinta.
"Mun damu matuka ganin yadda tun da ta shiga ofis, Misis Mary Alile-Idele ta nuna rashin kwarewa, alamu sun nuna kasuwancinta ta sa a gaba ba jam'iyyar APC ba.
"Muna da shaidar yadda take yawo zuwa jihohi domin rantsar da shugabannin ƙungiyarta mai zaman kanta (NGO) maimakon a ganta tana tallata manufofin APC ga mata."
“Duba da ɗimbin kuskurenta da rashin da’a, muna kira da a gaggauta tsige ta daga jam’iyyar APC. Ta nuna ba za ta iya ba kuma mu mun gaji haka nan."
Shugabar matan Imo ta kare Alile-Idele
Sai dai Misis Patricia Okuebor-Benson, shugabar matan APC ta jihar Imo, ta shiga sahun masu kare Alile-Idele, inda ta ce zargin ba gaskiya ba ne.
“Ba mu san daga ina waɗannan matan suke samun labaransu ba. Ina ganin wani ne ke daukar nauyinsu."
Za a fara sauraron ƙarar Ganduje
A wani rahoton kuma babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta tsayar da ranar da za ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan Abdullahi Umar Ganduje.
Alƙalin kotun mai shari'a Inyang Ekwo ya sanya ranar, 13 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙarar wacce ke neman a tsige Ganduje daga shugabancin APC.
Asali: Legit.ng