Shekara 1 a Ofis: Jerin Ministoci 10 da Suka Fi Kowa Kokari a Gwamnatin Tinubu

Shekara 1 a Ofis: Jerin Ministoci 10 da Suka Fi Kowa Kokari a Gwamnatin Tinubu

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi bikin cika shekara guda a kan karagar mulki a ranar Laraba 29 ga Mayu, 2024. Masu fashin baki sun tantance ministocin da suka fi ƙoƙari a gwamnatin APC.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Da suke jawabi a shirin siyasa na Channels TV, mai sharhi kan harkokin siyasa, Jide Ojo da babban darakta na cibiyar zabe ta Afirka Bell Ihua, Johnson Kolawole sun tantance ministocin.

Nyesome Wike ne kan gaba a jerin ministocin da suka fi kokari a gwamnatin Bola Tinubu
Jerin sunayen ministocin Bola Tinubu guda 10 da suka fi kowa yin aiki. Hoto: @BTOofficial, @officialABAT, @GovWike
Asali: Twitter

Manazartan sun zayyana sunayen ministocin gwamnatin tarayya da kuma wadanda suka yi fice a wajen gudanar da aikin su, kamar yadda gidan talabin ya wallafa.

A ƙasa ga jerin ministoci goma da suka fi kowa kokari a shekara daya:

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Tinubu ya bayyana dalilin kai gwamnonin jihohi 36 kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ministan Abuja, Nyesom Wike

An bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayin wanda ya fi kowanne minista a kokari a gwamnatin Tinubu a shekara daya da ta wuce.

Wike wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne, ya kammala wasu ayyuka da aka yi watsi da su a babban birnin Najeriya, wadanda shugaban kasar ya kaddamar a ranar Laraba.

2. Ministan harkokin gida, Olubunmi Tunji-Ojo

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda haifaffen jihar Ondo ne ya kasance minista na biyu mafi kokari a gwamnatin Tinubu a shekarar da ta gabata.

An tantance kokarin ministan ne bayan ya tabbatar da kammaluwar fasfo na sama da mutane 200,000 daga ma’aikatar harkokin cikin gida.

3. Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo

An bayyana sunan Festus Keyamo a cikin manyan ministoci goma da suka yi aiki tukuru a majalisar ministocin Tinubu a shekara daya da ta wuce.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dakatar da muhimmin aikin da Buhari ya fara a Najeriya

4. Ministan ayyuka, Dave Umahi

An kuma bayyana tsohon gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a matsayin daya daga cikin ministocin da suka fi yin aiki a cikin kwanaki 365 na gwamnatin Tinubu.

Umahi ya dage da gina tituna da aka hada su da kankare a fadin kasar nan kuma an gan shi yana duba ayyukan hanyoyin a wurare daban-daban.

5. Ministar ciniki da zuba jari, Doris Uzoka

Ministar kasuwanci da saka hannun jari ta kasance likita kuma kwararriya kan harkokin kudi kafin Shugaba Tinubu ya nada ta a matsayin mamba a majalisarsa.

Ma'aikatarta ta kafa tsare-tsaren bayar da tallafi da ga 'yan Najeriya a lokuta da dama tun lokacin da ta zama minista.

Sauran ministoci 5 masu kokari

6. Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Atiku Bagudu

7. Ministan tattalin arzikin teku, Gboyega Oyetola.

8. Ministan lafiya, Muhammed Ali-Pate

9. Ministan ma'adanai da albarkatun kasa, Dele Alake

Kara karanta wannan

Shekara 1 a mulki: 'Dan PDP ya bayyana sunayen gwamnoni 3 mafi taka rawar gani

10 Ministan sadarwa da fasahar tattara bayanai, Bosun Tijani.

Duba bidiyon tantacewa a nan kasa:

Kasashen Afrika da suka sauya taken kasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa kafin Najeriya ta sauya taken kasarta a makon nan, akalla kasashen Afrika 7 ne suka sauya taken kasar su a baya.

Rwanda, Afrika ta Kudu, na daga cikin jerin kasashen da suka sauya taken kasar ta su, kamar yadda muka tattara bayanai game da dalilin sauye-sauyen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.