Fubara v Wike: Gwamna Ya Bayyana Yadda Ya Shekara Yana Gwagwarmaya da Ubangida

Fubara v Wike: Gwamna Ya Bayyana Yadda Ya Shekara Yana Gwagwarmaya da Ubangida

  • Yayin murnar cika shekara daya a kan mulki, gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana yadda aka bar masa tarin bashi
  • Gwamna Fubara ya kuma bayyana dalilin da yasa tsohon gwamna Nyesom Wike ya fara yakarsa tun wata uku da zamansa gwamna
  • Har ila yau gwamnan ya bayyana irin nasarorin da ya samu da kalubalen da jihar ta fuskanta cikin shekara daya da ya yi yana shugabanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana yadda gwamnatinsa ta shafe shekara daya kan mulki.

Gwamna Fubara ya bayyana lamarin ne ga jami'an gwamnatinsa domin su san halin da ke ciki da kuma yadda za su fuskanci gaba.

Kara karanta wannan

Maganar Firaministan Birtaniya mai kama da ta Pantami ta tayar da kura a Intanet

Fubara
Gwamna Fubara ya bayyana yadda ya shekara cikin rikici a Ribas. Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Bashin da Wike ya bari a jihar Ribas

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamna Fubara ya koka kan tarin bashin da ministan Abuja ya bari a jihar bayan shafe shekaru takwas yana gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fubara ya ce ya gaji ayyuka 34 da ba a ƙarasa ba kuma kuɗinsu ya kai sama ba Naira biliyan 200.

Wike ya hana gwamna Fubara zaman lafiya

Gwamna Fubara ya kuma bayyana cewa gwamna Wike ya fara yakarsa tun wata uku da fara mulki saboda ya nuna ƙoƙarin kare martabar mutanen jihar.

Fubara ya ce amma bai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa ya kare muraɗin mutanen jihar kuma yanzu ya yi maganin Wike.

Gwamna Fubara ya cika alkawuransa?

Gwamnan ya yi ikirarin cika alkawuran da ya yi a lokacin zabe musamman a ɓangarorin kiwon lafiya, noma da ilimi, rahoton the Nation.

Kara karanta wannan

Jirgin kasa ya yi hadari a Abuja, ya latse jariran tagwaye sun mutu

Fubara ya ce ya gaji tattalin arziki marar kan gado daga Wike amma a cikin shekara daya ya dawo da tattalin jihar kan hayyacinsa.

Tinubu ya canza taken Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya canza taken Najeriya a lokacin da ya cika shekara daya da hawa karagar mulki.

Sai dai sabon taken bai samu karbuwa yadda ya kamata a wurin 'yan kasa ba kuma sun mayar da martani ga shugaban kasar a kafafen sada zumunta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel