Taken Najeriya: Hadimin Tsohon Shugaban Kasa Ya Caccaki Tinubu a Karon Farko
- Marubuci, Reno Omokri ya caccaki Bola Tinubu a karon farko bayan hawa mulki kan sauya taken Najeriya da ya yi
- Omokri ya ce kwata-kwata wannan koma-baya ne kuma ba shi da amfani a wannan lokaci da ake cikin tarun matsalolin
- Wannan na zuwa ne bayan sauya taken Najeriya daga "Arise O Compatriot" zuwa "Nigeria We Hail Thee" a ƙasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon hadimin tsohon shugaba kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya magantu kan sabon taken Najeriya.
Fasto Reno Omokri ya ce babban kuskure ne dawo da tsohon taken Najeriya a yanzu inda ya ce hakan koma baya ne.
Sabon taken Najeriya: Omokri ya soki Tinubu
Marubucin ya ce sabon taken Najeriya na yanzu ƴar ƙasar Burtaniya ce ta rubuta yayin da wanda aka sauya kuma matasan Najeriya suka tsara shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya koka kan yadda Tinubu ya dauki wannan mataki yayin d ya shawarce shi da ya mayar da ita "Arise O Compatriot".
"Raina ya baci, a ra'ayina wannan baban koma-bayan ne ga Najeriya."
"Ka da ku ga laifina na goyi bayan tsare-tsaren wannan gwamnati da dama da suka haɗa da cire tallafi da sauran tsare-tsare."
"Wannan abin kwata-kwata bai kamata a wannan lokaci ba, mene matsalar taken Najeriya da aka sauya? Ya tabbata muna mantawa da matsalolin da muke ciki a yanzu."
- Reno Omokri
Tinubu ya tabbatar da sabon taken Najeriya
Wannan na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sauya taken Najeriya daga "Arise O Compatriot" zuwa "Nigeria We Hail Thee".
Ƴan Najeriya da dama sun kushe wannan mataki inda suke ganin bashi da wani amfani a wurin ƴan kasar.
Abubuwa 6 game da sabon taken Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa a yau shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sauya taken Najeriya da yanzu ake yi.
Akwai jerin abubuwa masu muhimmanci game da sabon taken Najeriya da aka ƙaƙabawa ƴan Najeriya a cikin wannan rahoto.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng