Buhari Ya Taya Bola Tinubu Murnar Cika Shekara 1 a Mulki, Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Najeriya

Buhari Ya Taya Bola Tinubu Murnar Cika Shekara 1 a Mulki, Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Najeriya

  • Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan madafun iko a Najeriya
  • Tsohon shugaban ƙasar ya yi kira ga ƴan Najeriya su goyi bayan gwamnatin Tinubu a koƙarinta na kawo ci gaban ƙasa
  • Tinubu ya karbi ragamar mulkin Najeriya daga hannun Buhari ranar 29 ga watan Mayu, 2023 bayan lashe zaɓen shugaban ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Daura, Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya magajinsa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara ɗaya a mulki.

Buhari ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya su marawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu baya domin ta samu nasara.

Kara karanta wannan

"Kano ta kama hanyar kamawa da wuta," Jigo ya buƙaci Tinubu ya dakatar da Gwamna Abba

Buhari da Tinubu.
Muhammadu Buhari ya yiwa Tinubu fatan samun nasara bayan ya cika shekara 1 a ofis Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Muhammadu Buhari da Bola Tinubu

A rahoton Channels tv, an ji cewa Tinubu ya karbi mulki daga hannun jigon jam'iyyarsa, Muhammadu Buhari a ranar 29 ga Mayu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekara guda bayan hawa kan madafun iko, Muhammadu Buhari ya aike da saƙon murna da fatan nasara ga Shugaba Tinubu da ya gaje shi.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da tsohon kakakin shugaban ƙasa, Mallam Garba Shehu ya fitar ranar Talata, 28 ga watan Mayu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Buhari ya tura saƙo ga ƴan Najeriya

Buhari ya yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su haɗa kai wuri guda kuma su zama masu fatan alheri ga ƙasarsu tare da yi wa gwamnatin Tinubu addu'ar nasara.

Ya kuma yi kira gare su da su ba gwamnatin Shugaba Tinubu haɗin kai da goyon baya domin ta samu nasara a kokarinta na gina Najeriyar da muke fata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya

A sanarwar, Mallam Garba Shehu ya ce:

"Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su ci gaba da haɗa kansu da ƙara danƙon zumunci tare da fatan alheri.
"Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya su taru su bai wa gwamnatin Tinubu goyon bayan da take buƙata domin samun nasara a kokarinta na gina Najeriyar da kowa ke fata.
"A karshe Buhari ya yiwa gwamnatin Bola Tinubu fatan alheri da kammala wa'adi cikin nasara."

'Ya kamata Tinubu ya magance rikicin Kano'

A wani rahoton na daban, an ji Ɗanbalki Kwamanda ya yi kira ga Bola Tinubu ya sa baki a rikicin sarautar Kano tun kafin gwamnati ta kafa tarihi mara kyau.

'Dan siyasar ya ce jihar Kano ta kama hanyar kamawa da wutar rikici matukar shugaban ƙasa bai gaggauta taka wa abin birki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel