Majalisar Dattawa Ta Gafartawa Sanata Abdul Ningi, Ta Fadi Matakin Gaba

Majalisar Dattawa Ta Gafartawa Sanata Abdul Ningi, Ta Fadi Matakin Gaba

  • Majalisar Dattawa ta yi zama kan Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi inda ta dauki matakin yi masa afuwa
  • Majalisar ta bayyana amfanin Ningi da kuma kwarewarsa tare da gudunmawar da yake bayarwa maras misaltuwa
  • Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ce matakin da suka dauka na dawo da Ningi ya wuce maganar kabilanci ko addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa a Najeriya ta yiwa Sanata Abdul Ningi afuwa bayan dakatar da shi na tsawon watanni uku.

Majalisar ta kuma bukaci sanatan ya dawo bakin aiki bayan dakatar da shi a ranar 12 ga watan Maris din wannan shekara da muke ciki.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cin kwakwa, Majalisa ta sauya taken Najeriya, ta fadi amfaninsa

Majalisar Dattawa ta yi afuwa ga Sanata Abdul Ningi
Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Abdul Ningi ya dawo bakin aiki bayan yi masa afuwa. Hoto: Godswill Akpabio, Abdul Ningi.
Asali: Facebook

An yafewa Abdul Ningi a Majalisar Dattawa

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar, Sanata Abba Moro shi ya gabatar da haka a yau Talata 28 ga watan Mayu, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Moro ya ce dakatar da Abdul Ningi abin takaici ne inda ya ce ya dauki nauyin dukkan abin da sanatan ya aikata, TheCable ta tattaro.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio shi ya bayyana sake kiran Ningi Majalisar bayan kiraye-kiraye da roko daga mambobin Majalisar.

Akpabio ya bayyana amfanin Ningi a Majalisa

Akpabio ya bayyana irin amfanin Ningi da gudunmawar da ya ke bayarwa saboda kwarewarsa.

Shugaban Majalisar ya ce matakin dawo da Ningi ta wuce maganar addini ko kabilanci inda ya kara jaddada himmatuwar majalisar wurin hadin kan yan kasa.

Wannan na zuwa ne makwanni biyu kafin wa'adin dakatarwar sanatan na watanni ta cika a watan gobe.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kau da kai ga rikicin sarautar Kano, zai yi jawabi a majalisun Tarayya a Abuja

Ana sa ran sanatan zai cika wa'adin dakatar da shi a ranar 12 ga Yunin wannan shekara ta 2024 da muke ciki.

Majalisar Dattawa ta sauya taken Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta tabbatar da kudirin dawo da tsohon taken Najeriya domin kara kishin ƙasa.

Majalisar ta amince da kudirin bayan ta tsallake karatu na uku a yau Talata 28 ga watan Mayun wannan shekara.

Tahir Monguno daga jihar Borno shi ya gabatar da kudirin inda ya ce wannan mataki ne mai matukar muhimmanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel