"Kano Ta Kama Hanyar Kamawa da Wuta," Jigo Ya Buƙaci Tinubu Ya Dakatar da Gwamna Abba
- Ɗanbalki Kwamanda ya yi kira ga Bola Tinubu ya sa baki a rikicin sarautar Kano tun kafin gwamnati ta kafa tarihi mara kyau
- Ya ce jihar Kano ta kama hanyar kamawa da wutar rikici matukar shugaban ƙasa bai gaggauta taka wa abin birki ba
- Ɗan siyasar ya ce yana mamakin yadda Abba Yusuf ya sa ƙafa ya shure umarnin kotu ya manta cewa kotu ce ta tabbatar masa da nasara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Alhaji Abdulmajid Danbilki-Kwamanda ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya takawa Gwamna Abba Kabir Yusuf birki.
Danbilki Kwamanda ya bukaci Tinubu ya dakatar da gwamnatin Kano tun kafin ta kafa mummunan tarihi a zamanin mulkinsa.
Sanusi II: Danbilki ya taso gwamna Abba
Abokin siyasar na tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Danbilki Kwamanda ya faɗi haka ne yayin zantawa da menama labarai kan rikicin sarautar Kano ranar Talata.
Ya gargaɗi shugaba Tinubu kar ya bari gwamnatin Kano ta fake da wasu dokokin jihar wajen saɓa umarnin kotu da ta hana mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.
An take doka wajen nada Sarkin Kano?
A cewarsa, abin da gwamnatin Kano ta aikata ya ci karo da umarnin babbar kotun tarayya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
A kalamansa ya ce:
"Abin da gwamnatin Kano ke yi ya saɓawa umarnin babbar kotun tarayya wanda ta hana dawo da Muhammadu Sanusi II, tana kokarin kafa mummunan tarihin da zai shafi kowa.
"Na kasa fahimtar yadda gwamnatin da kotu ta kafa, a yanzu ta dawo tana neman sa ƙafar wando ɗaya da umarnin kotun wacce ke ƙoƙarin hana ta aikata kuskure.
"Mu ajiye siyasa a gefe, ƙoƙarin ƙaƙaba sabon sarkin da aka dawo da shi a matsayin shi ne sahihin sarkin Kano barazana ce ga kundin tsarin mulki da zaman lafiya."
Kano: Ya kamata Tinubu ya sa baki
Ɗanbalki Kwamanda ya buƙaci shugaban ƙasa ya gaggauta sa baki kan rikicin da ke faruwa domin dawo da zaman lafiya a jihar Kano, cewar Daily Post.
“Muna kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya gaggauta yin abin da ya dace ya tsoma baki a cikin lamarin domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar," in ji shi.
Yan sanda sun shirya tsaf a Kano
A wani rahoton kuma, an ji yan sanda sun shirya ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da fitina a jihar Kano yayin da ake taƙaddamar sarauta
CP Usaini Gumel, kwamshinan ƴan sandan jihar ya ce ba za su lamunci wasu tsiraru su ruguza zaman lafiyar da ake da ita a Kano ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng