2027: Jam’iyyun Adawa Na Shirin Hadaka a Doke APC, Peter Obi Ya Bayyana Sharudda
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya yi karin haske kan maganar hadakarsa da Atiku Abubakar
- Peter Obi ya ce matuƙar aka samu daidaito kan yadda za a magance matsalolin Najeriya a tsakaninsu zai goyi bayan haɗakar
- Legit ta tattauna da wani dan jam'iyyar PDP, Aminu Abubakar domin jin yadda yake ga hadakar za ta samar wa jam'iyyun adawa nasara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour a zaben da ya wuce, Peter Obi ya bayyana dalilan da za su sa shi yin haɗaka da PDP a 2027.
Peter Obi ya hadu da 'yan jarida
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Peter Obi ya bayyana haka ne a yayin hira da ya yi da yan jarida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin na Peter Obi na zuwa ne bayan wata ziyara da ya kai wa Atiku Abubakar da wasu manyan yan jam'iyyar PDP a kwanakin baya da kuma kiran da Atiku ya yi kan haɗaka tsakaninsu.
Atiku Abubakar zai goyi bayan Peter Obi?
A kwanakin baya ne tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce idan har aka mika tikitin takarar PDP zuwa kudu maso gabashin Najeriya to zai goyi bayan Peter Obi.
Peter Obi ya yi godiya ga Atiku Abubakar bisa wannan bayani da ya yi kuma ya ce hakan ya kara masa karfin gwuiwa kan yin haɗaka tsakaninsu.
Sharuddan hadakar Peter Obi-Atiku Abubakar
Sai dai a cikin hirar da Peter Obi ya yi, ya bayyana cewa dole ne hadakar ta kasance kan ceto Najeriya a halin da take ciki.
Amma ya ce idan dai kawai za a yi haɗakar ce domin samun damar tsayawa takara a zaɓen 2027 to shi ba zai goyi bayanta ba.
"Peter Obi ba mayen mulki ba ne"
Har ila yau Peter Obi ya bayyana cewa shi ba wanda ya damu da dole sai ya mulki Najeriya ko ta halin ƙaƙa ba ne, rahoton the Cable.
Ya ce shi yana siyasa ne domin ganin ya share wa yan Najeriya hawaye da kawo ayyukan cigaban ƙasa musamman wadanda suka shafi talakawa.
Legit ta tattauna da Aminu Abubakar
Wani dan jam'iyyar PDP, Aminu Abubakar ya zantawa Legit cewa lallai hadakar ita ce mafita ga jam'iyyun adawa a Najeriya.
Ya ce idan aka hada kuri'un da jam'iyyun adawa suka samu a zaben 2023 yafi yawan kuri'un da Bola Tinubu ya samu, saboda haka idan suka hadu za su kayar da APC cikin sauki.
Utomi ya nemi hadakar LP da PDP
A wani rahoton, kun ji cewa jigon siyasa a Najeriya ya bayyana yiwuwar kirkirar sabuwar jam’iyya a Najeriya da ‘yan siyasa za su yi kafin zabe.
Pat Utomi ya ce, akwai bukatar a hada kai tsakanin ‘yan siyasa domin samun shugabanni na gari bayan mulkin APC domin ciyar da kasa gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng