Kotu Ta Watsawa APC Kasa a Ido, Ta Tabbatar da Diri a Matsayin Gwamnan Bayelsa
- Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da sake zaben gwamna Douye Diri na Bayelsa
- Mai shari’a Adekunle da ke jagorantar kotun mai mutane uku a ranar Litinin ya kori karar da APC ta shigar saboda rashin cancanta
- Kotun ta ce APC ta gaza kare zarge-zargen da ta ke na cewa an tafka kura-kurai a zaben gwamnan jihar da aka gudanar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Bayelsa ta tabbatar da nasarar sake zaben Douye Diri a matsayin gwamnan jihar.
cKotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Adekunle Adeleye, ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC da dan takararta Timipre Sylva suka shigar saboda rashin cancanta.
Kotu ta yi watsi da karar APC
A hukuncin da kotun ta yanke a yau Litinin, ta ce wadanda suka shigar da karar sun gaza gabatar da kwakkwaran hujjoji, in ji rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a Adekunle Adeleye a madadin kotun ya ce APC ta gaza kare zarge-zargen da ta ke na cewa an tafka kura-kurai a zaben gwamnan jihar da aka gudanar.
Jaridar The Nation ta ruwaito kotun ta yi watsi da duk wasu ƙarin shaidu da kuma jawaban rantsuwar da wasu shaidun da suka gabata suka bayar a kan ƙarar.
Kotu ta zargi APC da yin jinkiri
A cewar kotun, doka ta bayyana karara cewa dole ne a shigar da karar zabe akalla bayan kwanaki 21 da bayyana sakamakon zaben.
Ta ce dole ne idan za a gabatar da irin wannan karar ya zamana an hada da dukkanin jawabai a rubuce da ya hada da jawaban dukkanin shaidun da za a gabatar, rahoton Tribune.
Amma kotun ta zargi APC da dan takararta Sylva na yin jinkiri wajen gabatar da jawaban shaidunta da kuma karin hujjoji.
Asali: Legit.ng