"Babu Ɗaga Ƙafa": An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Tsige Wasu Ministoci Daga Muƙamansu

"Babu Ɗaga Ƙafa": An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Tsige Wasu Ministoci Daga Muƙamansu

  • An buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kori duk ministan da aka gano ya gaza sauke nauyin da aka ɗora masa
  • Wata ƙungiya mai zaman kanta ta ce za ta fara tantance ayyukan ministocin gwamnatin Bola Tinubu domin gano masu dumama kujera
  • Ta kuma bayyana ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike a matsayin gwarzon ministoci na wannan watan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wata ƙungiyar fararen hula (CSO) ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kori ministocin da suka gaza sauke nauyin da aka ɗora masu.

Kungiyar ta ƴan gwagwarmaya 'Stay Alert Human Right Awareness Initiative' ta buƙaci Tinubu ya kori duk wanda ba zai iya aikin da aka ɗora masa ba a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Kungiyar fararen hula ta buƙaci Bola Tinubu ya kori wasu ministoci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ta kuma sha alwashin cewa za ta sa ido kan ayyukan kowace ma'aikata kuma a shirye take ta soki duk wanda ya gaza kuma za ta ba da shawarin a kore shi daga aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar Ambasada Lary Onah ne ya yi wannan kira yayin zantawa da manema labarai a Abuja, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ƙungiyar za ta binciki ministocin Tinubu

Ya bayyana cewa za su gudanar da binciken kwa-kwaf kan duk wanda aka naɗa a gwamnati domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.

"Tun da aka kafa ƙasar nan ba ta taɓa rasa kyawawan manufofi da tsare-tsare ba, sai dai rashin bin diddigi da sa ido kan aiwatar da kasafin kuɗi da manyan ayyuka'"

- Larry Onah.

Ya ambaci abubuwan da yake hangen sune ke kawo koma baya a ƙasar nan da suka haɗa da cin hanci da rashawa, rashin kishin ƙasa, rashin sa ido da bin diddigi.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya fadi ainihin lokacin da ya fara mulkin jihar Rivers

Mista Onah ya ce ƙungiyarsu za ta fara tantance ayyukan ministoci duk wata domin kara masu azama da jajircewa.

Ministan Abuja ya zama gwarzon wata

Yayin da yake yabawa da ƙoƙarin wasu ministocin, shugaban ƙungiyar ya ayyana ministan Abuja, Nyesom Wike, a matsayin gwarzon ministoci na wannan watan.

Kungiyar ta yaba da kokarin Wike wajen tabbatar da kyawawan tituna, ƙarasa ayyukan gina tituna, inganta tsaro, wanda hakan ya sa Abuja ta zama wuri mai aminci.

Idan bak u manta ba Shugaba Tinubu ya gargaɗi ministocin da naɗa cewa ba zai lamurci gazawa ba kuma a shirya yake ya kori duk wanda ba zai iya ba, The Cable ta ruwaito.

NLC ta ja daga da gwamnatin Tinubu

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta sake gamuwa da cikas daga ƴan kwadago bayan ta gabatar da tayin N57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Rahotanni sun nuna ƴan kwadago a Najeriya sun yi fatali da tayin a karo na uku amma sun rage bukatarsu daga N615, 000 zuwa N497,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel