'Ba 'Yan Jam'iyya ba ne,' Matasan APC sun yi Martani ga Masu Son a Tsige Abdullahi Ganduje

'Ba 'Yan Jam'iyya ba ne,' Matasan APC sun yi Martani ga Masu Son a Tsige Abdullahi Ganduje

  • Matasan jam'iyyar APC a karkashin kungiyar Youth Solidarity Network, sun barranta jam'iyyar daga masu fafutukar a raba Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar
  • Shugaban kungiyar, Prince Danesi Momoh ne ya bayyana haka ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce da yawansu ba 'yan jam'iyya ba ne
  • Ya koka kan yadda mutanen da ya bayyana da baragurbin 'yan jam'iyya su ka karbo kwangilar ta hanyar kokarin kawo rudani gabanin zaben shekarar 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Kungiyar matasan APC na kasa sun barranta kansu da masu fafutukar tsige shugaban jam'iyyar na Kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Ganduje: Shirin tsige shugaban APC na ƙasa da maye gurbinsa ya gamu da cikas

A 'yan kwanakin nan ana jiyo wasu 'yan APC a shiyyar Arewa maso gabas suna neman hadin kan shiyyar Yamma domin raba Abdullahi Ganduje da kujerersa.

Abdullahi Umar Ganduje
Matasan APC sun bayyana masu son a cire Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC da bara-gurbi Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Leadership News ta wallafa cewa kungiyar matasan jam'iyyar ta ce wadanda ke wannan kokari bara gurbin 'yan jam'iyya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana kokarin cire Abdullahi Ganduje a matsayin wani yunkuri na karkatar da hankalin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu daga ayyukan da ya ke yi ga ‘yan kasa.

Matasan APC sun goyi bayan Ganduje

Shugaban kungiyar matasan jam’iyyar APC na Youth Solidarity Network, Prince Danesi Momoh ya jaddada goyon bayansu ga shugabancin Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar.

Shugaban ya shaidawa ‘yan jarida a Abuja cewa makiyan jam’iyyar APC ne kawai ke son kawo rudani, kuma biyansu aka yi domin rikita jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Babu ruwan NLC da zancen hadewar Atiku da Obi', Kungiyar kwadago za ta kawo cikas

The Gazelle News ta wallafa cewa matasan na ganin cire Abdullahi Umar Ganduje zai kawo babban nakasu a kakar zaben 2027.

A kalamansa;

“Mun gano cewa masu fafutukar sai an cire Abdullahi Umar Ganduje ba ‘yan jam’iyyar APC ba ne. Sojojin haya ne da aka biya su domin kawo rudani a cikin jam’iyyar.’

2027: APC na kokarin karbe wasu jihohi

A baya mun kawo mu ku labarin cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa suna shirye-shiryen karbe wasu jihohi a zaben gaba.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne a wurin bikin taron cikar shugaba Bola Ahmed Tinubu shekara daya a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel