'Yan APC Sun Fadi Wadanda Suka Sanya Su Yin Zanga Zangar Adawa da Ganduje

'Yan APC Sun Fadi Wadanda Suka Sanya Su Yin Zanga Zangar Adawa da Ganduje

  • Ƙungiyar APC Youth Solidarity Network ta ce yaudararsu aka yi domin su yi zanga-zangar nuna adawa da Dr. Abdullahi Umar Ganduje
  • 'Yan siyasar sun ce maƙiyan jam’iyyar APC ne suka sanya su yi zanga-zangar neman Ganduje ya sauka daga muƙaminsa na shugaban jam’iyyar
  • Sun bayyana cewa sun gane kura-kuransu don haka suka buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da cewa ba a tsige Ganduje daga kujerar ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar APC Youth Solidarity Network ta bayyana cewa maƙiyan jam’iyyar ne suka ɗauki nauyinsu domin gudanar da zanga-zangar neman tsige Abdullahi Umar Ganduje.

Jagoran ƙungiyar na ƙasa, Prince Danesi Momoh, ya ce waɗanda ke haɗa kai da jam’iyyar NNPP ne suka yaudare su domin kawo cikas ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Zamu karɓe wasu jihohi," Ganduje ya bayyana abubuwa 2 da APC ta shirya a 2027

Kungiyar APC sun yi amai sun lashe kan zanga-zangar Ganduje
Kungiyar ta ce yaudararsu aka yi domin yin zanga-zanga kan Ganduje Hoto: APC Youth Solidarity Network
Asali: UGC

Danesi Momoh ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Talata, 21 ga watan Mayu wacce Legit.ng ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa suka yaudari ƴan ƙungiyar APC?

Ƙungiyar ta ce waɗanda ke ƙorafin rashin samun mafaka a gwamnatin Tinubu na fakewa da batun dakatarwar domin kawo hargitsi a jam'iyyar.

A kalamansa:

“An yaudare mu cewa hanya ɗaya tilo da za mu ceci jam’iyyarmu, ita ce ta neman tsige Ganduje, domin gudun kaucewa abin da ya faru a Zamfara, inda APC ta ci zaɓe amma daga baya aka ba jam'iyyar adawa nasara a Kotun Ƙoli."

Wane kira suka yi ga Tinubu?

Jagoran na jam’iyyar APC ya yi kira ga Tinubu da ya tabbatar da cewa Ganduje ya ci gaba da riƙe mukamin shugaban jam'iyyar na ƙasa.

“A namu bangaren, za mu gudanar da zanga-zangar haɗin gwiwa domin shaida wa duk masu fada a ji cewa babu wani gurbi a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa, kuma ko me za su yi, Ganduje zai kammala wa’adinsa."

Kara karanta wannan

Ganduje: Shirin tsige shugaban APC na ƙasa da maye gurbinsa ya gamu da cikas

"Mu ne muka fara zanga-zangar adawa da shugaban jam’iyyar na ƙasa kuma mun ba da haƙuri da muka bari aka yi amfani da mu kan jam'iyyarmu. Za muyi aiki tare da shugaban jam'iyyar na ƙasa domin ciyar da jam’iyyarmu gaba.”

- Prince Danesi Momoh

An ba Abdullahi Ganduje shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ba shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, shawara kan rikicin jam'iyyar.

Abbas Tajudeen ya buƙaci Ganduje da ya kafa kwamitocin sulhu da za su haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar da ke rikici da juna a faɗin ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel