Ribas: Minista ya gamu da matsala yayin da kotu ta soke dokar tsawaita wa'adin ciyamomi 23

Ribas: Minista ya gamu da matsala yayin da kotu ta soke dokar tsawaita wa'adin ciyamomi 23

  • Kotun jihar Ribas mai zama a Fatakwal ta yanke hukunci kan sahihancin tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi 23
  • Hakan ya biyo bayan dokar da ƴan majalisa 27 na tsagin Wike suka amince da da ita na ƙarawa ciyamomi watanni shida
  • A zaman yau Talata, kotun ta bayyana ƙarin a matsayin haramun saboda ya saɓawa tanadin dokar ƙasa da ta jihar Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Babbar kotun jihar Ribas mai zama a Fatakwal ta soke ƙarin wa'adin da aka yi wa shugabannin kananan hukumomin jihar 23.

Kotun ta kuma ayyana dokar ƙananan hukumomi mai lamba 2, 2024 wadda ta tsawaita wa'adin ciyamomi da watanni shida a matsayin mara inganci.

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

Gwamna Sim Fubara na Rivers.
Kotun ta soke dokar tsawaita wa'adin ciyamomi da kansiloli a jihar Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Yadda aka ƙara wa'adin ciyamomin Rivers

Tun farko dai ƴan majalisa 27 da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, sun amince da dokar ƙarawa ciyamomin wa'adin watanni uku, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisar sun ɗauki wannan matakin ne a daidai lokacin da alaƙa ta ƙara tsami tsakanin tsagin Wike da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas.

Dokar kananan hukumomi mai lamba 2 da ƴan majalisar suka amince da ita, ta tsawaita wa'adin ciyamomi da kansiloli da watanni shida.

Kotu ta soke ƙarin wa'adin

Amma yayin da take yanke hukunci kan lamarin ranar Talata, babbar kotun Ribas ta ce dokar tsawaita wa'adin ciyamomin ta saɓawa kudin tsarin mulki 1999.

Haka zalika kotun ta ce ƙara wa shugabannin ƙananan hukumomin wa'adi bayan kammala shekaru uku ya saɓawa ka'ida duba da sashe na 9 (1) na dokar jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya shirya zai tsamo sama da mutane 7,000 daga ƙangin rashin aikin yi

Legit Hausa ta gano cewa kundin dokokin jihar Ribas ya kayyade cewa duk zaɓaɓɓen ciyaman da kansila zai shafe shekaru uku a mulki, daga nan kuma za su sauka.

A rahoton The Nation, kotun ta ƙarƙare da cewa ƙarin wa'adin da aka yi wa ciyamomin kwanan nan bai halatta ba.

Honorabul Enyiada Cookey-Gam da wasu mutum shida ne suka shigar da karar, inda suka kalubalanci gwamnan jihar a ƙara mai lamba PHC/1320/CS/2024.

Kotun ta tabbatar da cewa wa’adin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli na nan a shekaru uku kamar yadda doka ta 2018 ta tanada.

Rivers: Kotu ta kori ƴan majalisa 27

A wani rahoton ƴan majalisa 27 da ke goyon bayan ministan Abuja sun shiga matsala yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ya dawo ɗanye.

Babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta hana ƴan majalisa 27 bayyana kansu a matsayin mambobin majalisar Ribas har sai ta yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Ana murnar Notcoin ya fashe, kotun tarayya ta yanke hukunci kan jami'in Binance a Najeriya

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel