Atiku Abubakar Ya Faɗi Dalilin da Zai Sa Ya Goyi Bayan Peter Obi a Zaben 2027

Atiku Abubakar Ya Faɗi Dalilin da Zai Sa Ya Goyi Bayan Peter Obi a Zaben 2027

  • Atiku Abubakar ya ce zai marawa Peter Obi baya b tare da shakkar komai ba idan PDP ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba zai yi jayayya da jam'iyyar PDP matuƙar ta zaɓi bai wa ɗan Kudu maso Gabas takara
  • Ya ce ko a zaɓen 2023 ya nemi takara ne saboda babbar jam'iyyar adawa ta buɗe kofa ga kowane mamba idan yana sha'awar takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai marawa Peter Obi baya idan har jam'iyyar PDP ta yanke shawarar tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2023, ya ce ba abin da zai hana ya goyi bsyan Obi matuƙar jam'iyyar ta miƙa tikitin takara zuwa Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

Obi tare da Atiku Abubakar.
Atiku ya tabbatar da cewa zai marawa Obi bayan idan PDP ta ba shi takara a 2027 Hoto: @Atiku
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Atiku ya nemi takara a 2023?

Ya kuma bayyana cewa ya shiga tseren neman tikitin takarar shugaban ƙasa a bara ne saboda PDP ta buɗe ƙofa ga kowane yankin Najeriya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Atiku na cewa:

"Na sha nanata cewa idan PDP ta yanke miƙa takara ga shiyyar Kudu maso Gabas ba zan nemi takara ba, ko a zaɓen 2023 na nanata wannan kalaman, matukar PDP ta yanke zan yi mata ɗa'a.
"To amma na shiga takarar tikitin shugaban ƙasa ne saboda jam'iyya ta buɗe kofa ga kowane mamba. Idan jam'uyya ta ce yanzu lokacin Kudu maso Gabas ne kuma aka zaɓi Obi, zai mara masa baya."

Atiku da Peter Obi za su dunƙule

Kara karanta wannan

Ganduje: Wasu ƴan Arewa sun kunno wuta kan kujerar shugaban APC na Ƙasa

Wazirin Adamawa ya ƙara da cewa akwai yiwuwar haɗa maja tsakanin PDP da jam'iyyar LP, yana mai cewa jam'iyyar PDP ce kaɗai za ta yanke makomarsa a siyasa.

Atiku ya ce ganawar da ya yi da Peter Obi kwanan nan wata alama ce da ke nuna akwai yiwuwar za su haɗa kansu gabanin babban zaɓen 2027.

Wani mamban PDP a Katsina, Kabir Abdullahi, ya ce wannan haɗa kan na Atiku da Obi, idan ta yiwu da Kwankwaso zai iya kawo ƙarshen mulkin APC a 2027.

Kabir ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa idan PDP ta tsayar da Peter Obi, ta haɗa shi da wani fitacce a Arewa, to komai ka iya faruwa duba da kuri'un da Obi ya samu a 2023.

A kalamansa ya ce:

"Wannan kalamai na Atiku sun nuna cewa shi dattijo ne, mu dama PDP muke yi duk wanda ya barta zamu raba gari da shi, muna fatan jam'iyya ta ɗauƙo wanda zai iya kayar da Tinubu.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Atiku ya bayyana matsayarsa kan sake neman takarar shugaban ƙasa a 2027

"Misali idan aka ba Obi takara, to a samu ɗaya cikin ukun nan a haɗa su, Kwankwaso, El-Rufai ko gwamnan Bauchi. Ina ganin za su iya samun nasarar daƙile Tinubu."

A cewarsa, ya kamata Kwankwaso ya haƙura ya dawo PDP a haɗu a ƙwato ƙasar nan daga hannun wannan jam'iyya ta APC.

Magoya bayan APC sun soki kwancen PDP-LP

A wani rahoton kuma Ƙungiyar NPH mai goyon bayan APC ta mayar da martani kan yunkurin ƴan adawa na haɗa maja gabanin zaɓen 2027.

Shugaban NPH, Hon. Bukie Okangbe ya ce babu wani kawance da ƴan siyasa za su ƙulla wanda zai kawo ƙarshen mulkin APC a zaɓe na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262