Dala vs Naira: Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Tinubu Ya Kori Gwamnan CBN da Minista 1

Dala vs Naira: Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Tinubu Ya Kori Gwamnan CBN da Minista 1

  • An buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tsige gwamnan CBN, Yemi Cardoso, da ministan kuɗi da tattalin arziki, Wale Edun
  • Babban jigo a jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju ne ya yi wannan kiran yayin wata hira ta musamman da Legit.ng, ya ce babu dalilin hana Crypto
  • A cewar ɗan siyasar, kamfanonin hada-hadar kuɗin intanet sun jima suna aikinsu tun kafin zuwa gwamnatin Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

An buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kori gwamnan babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso, da ministan kudi kuma mai kula da tattalin arziƙi, Wale Edun.

Rilwan Olanrewaju, jigo a babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ne ya yi wannan kira yayin hira ta musamman da jaridar Legit.ng.

Kara karanta wannan

Ana murnar Notcoin ya fashe, kotun tarayya ta yanke hukunci kan jami'in Binance a Najeriya

Bola Tinubu, Cardoso da Wale Edun
Jigon PDP ya buƙaci Tinubu ya canza gwamnan CBN da ministan kuɗi Hoto: @OfficialABAT, @DrYemiCardoso
Asali: Twitter

Ya ce babu dalilin ɗaukar mataki kan manhajar hada-hadar kudin intanet watau Binance idan har gwamnan CBN da Mista Edun sun yi aikin da ya dace game da tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon PDP ya kuma soki jam'iyyar APC da cewa a kowane lokaci sai dai ta fito tana kukan an ɓata kaza da kaza maimakon kawai ta fito ta ɗauki nauyi.

Ya ƙara da cewa manhajar Binance ta ɗauki tsawon lokaci tana gudanar da harkokinta a Najeriya, don haka bai kamata a ɗorawa kamfanin Crypton alhakin karyewar Naira ba.

Jigon PDP ya soki APC kan karyewar Naira

Olanrewaju ya ce gwamnatin APC ta maida hankali wajen yaƙar iyayen da ke tura ƴaƴansu makarantun ƙasashen waje, ƴan canji da sauran su.

A cewarsa, maimakon wannan rigimar da gwamnatin APC ke yi da su, kamata ya yi ta bullo da tsare-tsaren tattalin arziƙi da za su farfaɗo da ƙimar kuɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da biyan bashin maƙudan tiriliyoyin kuɗi da ake bin Najeriya

A kalamansa ya ce:

"Mista Cardoso da Wale Edun, mutane ne da ba su da alƙibla, wadanda suka samu dama saboda uban gidansu ya yi magudi ya shige Aso Rock, ba wai don sun cancanta ba.
"Abin takaici ne ganin Shugaba Tinubu ya ɗora daga inda Buhari ya tsaya, a Najeriya ne za ka ga jami'an kuɗi suna ɓullo da tsare-tsare ƙarya, su ɗauki nauyin masu kumfar baki domin yaɗa farfaganda a a midiya.
"Binance ba ita ce matsalar ba, tun kafin su hau mulki Binance take aiki a Najeriya, sun zargi iyayen da ke tura ƴaƴansu karatu waje da ƴan canji, ina fatan ba za su ɗora wa Allah laifi ba nan gaba.
"Mafitar da ta rage ita ce shugaban ƙasa ya kori Cardoso da Edun kuma ya zaƙulo gogaggun da suka san harkar waɗanda za su zo da tsare-tsaren ceto Naira."

Tinubu ya fara biyan bashin Najeriya

A wani rahoton kuma Bola Tinubu ya ba da umarnin biyan bashin kuɗaɗen da ake bin ɓangaren wutar lantarki wanda ya haura N3.3trn.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa ya sauya sheƙa zuwa APC

Shugaban ƙasar ya amince a biya bashin a hankali a hankali domin magance matsalar rashin samun wutar lantarki a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel