Cin Amana: Bayan Caccakar Ministocin Tinubu, APC Ta Dakatar da Sanata Mai Ci a Jam'iyya
- Rikicin siyasa ya kara tsami a jihar Ondo bayan dakatar da Sanata Jimoh Ibrahim daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
- An dakatar da sanatan ne kan zargin cin amanar jami'yyar bayan zaben fida gwani da aka gudanar a jihar a kwanan nan
- Shugabannin jam'iyyar a gundumar Igbotako Ward 11 a karamar hukumar Okitipupa ne suka dauki wannan mataki kan sanatan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo ta dakatar da Sanata Jimoh Ibrahim kan zargin cin dunduniyarta.
Ana zargin Sanata Ibrahim da ke wakiltar Ondo ta Kudu a Majalisar Dattawa da saba dokokin jam'iyyar da kuma cin amana.
Matakin da APC ta dauka kan sanatan
Shugabannin jam'iyyar APC a gundumar Igbotako 11 a karamar hukumar Okitipupa a jihar su suka dauki wannan mataki, cewar Daily Post.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakardar da aka sanyawa hannu na dauke da sunayen shugabannin da suka haɗa da Bakere Usuf da Tore Obwoselu da Oloyinmi Idowu da kuma Borewaye Louyomi, cewar Tribune.
Sauran sun hada da Oladipupo Bose da Alkimbobola Seyi da Lawal-Babatunde da Aritawe-Ademole da Akinkuoju Olarewaju da kuma Fabioye Ajoke.
Sanata ya caccaki zaben fidda gwanin APC
Wannan dakatarwa na zuwa ne bayan sanatan ya rasa tikitin takarar gwamnan jihar da aka gudanar a Ondo.
Jimoh ya ce kwata-kwata ba a bi tsarin dokar jam'iyyar APC ba wurin ayyana wanda ya lashe zaben fidda gwani a jihar.
A kwanakin baya, Sanata Jimoh ya kalubalanci Ministocin Bola Tinubu inda ya bukaci a sallami da dama daga cikinsu kan rashin tabuka komai.
Sanata ya caccaki Ministocin Tinubu
A wani labarin, Mamban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Dattawa, Jimoh Ibrahim ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya kori wasu daga cikin ministocinsa.
Sanata Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi kan Majalisar ministoci da muƙarraban Tinubu yayin hira da yan jaridu.
Sanata Jimij mai wakiltar Ondo ta kudu, ya nuna damuwa kan cewa ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa a yanzu ba su da gogewar aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng