'Na Ziyarci Atiku, Lamido da Saraki, Amma Ina da Dalili', Peter Obi Ya Magantu
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labor, Peter Obi ya magantu kan ziyarar da ya kai wa jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP
- Peter Obi ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da wasu tsofaffin gwamnonin Arewa a farkon makon nan
- Mai taimakawa Peter Obi ne a harkokin sadarwa, Dakta Yunusa Tanko ya bayyanawa manema labarai makasudin ziyarce-ziyarcen
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 karkashin jami'yyar Labor, Peter Obi ya magantu kan ziyarar da ya kai wa jiga-igan jam'iyyar PDP.
Peter Obi ya ziyarci manyan PDP
Wadanda Peter Obi ya ziyarta sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ziyarar dai ta bar baya da kura dangane da makomar jam'iyyun adawa a babban zabe mai zuwa na shekarar 2027.
Mai taimakawa Peter Obi a harakokin sadarwa, Dakta Yunusa Tanko ya yi karin haske kan ziyarce-ziyarcen, cewar rahoton Vanguard.
Dalilin ziyarce-ziyarcen Peter Obi
Dakta Yunusa Tanko ya yi karin hasken ne jim kadan bayan Peter Obi ya kammala tattaunawa da shugabannin na PDP.
A cewar Dakta Tanko, babban dalilin ziyarar shine tattaunawa kan mummunan halin da Najeriya ke ciki.
Sai kuma halin da talakawa suka samu kansu a ciki na tsananin rayuwa, cewar rahoton jaridar Punch.
Ya kuma kara da cewa Peter Obi yana shirye a koda yaushe wurin ganin an samu cigaba da zaman lafiya a Najeriya.
Atiku Abubakar bai ce komai ba tukuna
Amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton bangaren Atiku Abubakar ba su magantu kan ziyarar ba.
Haka zalika mai taimakawa Atiku Abubakar a harkokin sadarwa, Paul Ibe ya ce bai samu bayani kan tattaunawar ba.
Alakar Atiku da Peter Obi a PDP
Atiku Abubakar da Peter Obi sun yi takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2019 karkashin jam'iyyar PDP.
Amma ba su samu nasara ba inda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kayar da su.
Masu sharhi suna kallon ziyarar a matsayin wani mataki da jam'iyyun adawa suke ƙoƙarin dauka domin kawo karshen mulkin APC a zaben 2027.
Peter Obi ya jinjinawa Atiku
A wani rahoton, kun ji cewa Peter Obi ya taya Atiku Abubakar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya jinjinawa jagoranci da gudunmawarsa wajen ci gaban Najeriya.
Peter Obi ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya domin taya Atiku murna, yana mai bayyana shi a matsayin babban yayansa kuma jagora mai mutunci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng