Tsohon Minista Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC, SGF Akume Ya Karɓe Shi a Abuja

Tsohon Minista Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC, SGF Akume Ya Karɓe Shi a Abuja

  • Tsohon ministan makamashi da ƙarafa, Farfesa Iyorwuese Hagher, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki a jihar Benuwai
  • Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya karɓi tsohon ministan a hukumance ranar Litinin a Abuja
  • Farfesa Hagher ya bayyana cewa yanzu ya samu nutsuwa domin ya dawo wurin da zai taimaki abokinsa, tsohon gwamna Akume

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya tarbi Farfesa Iyorwuese Hagher wanda ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).

Akume ya yi maraba da tsohon ministan zuwa jam'iyyar APC mai mulki a hukumance ranar Litinin, 13 ga watan Mayu a Abuja, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga muhimmin taro a Villa, ya rantsar da sababbin kwamishinoni 2

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
SGF George Akume ya karɓi tsohon ministan da ya sauya sheƙa zuwa APC a Abuja Hoto: Sen. George Akume
Asali: Twitter

SGF ya karbi Farfesa Hagher a APC

Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa Farfesa Hagher ya ɗauki miƙaƙƙiyar hanya yayin da ya fice daga PDP zuwa APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SGF ya halarci wurin bikin karɓan tsohon ministan tare da rakiyar majalisar dattawan APC ta jihar Benuwai ƙarƙashin jagorancin Simon Shango.

A ɗaya ɓangaren kuma Hagher ya samu rakiyar Msughve Ayua, wanda ya wakilci Honorabul Jonathan Agbidyeh, mamba mai wakiltar Katsina-Ala a majalisar dokokin Benue.

Alakar Akume da Hagher a siyasa

Hagher, Farfesa a fannin wasan kwaikwayo shi ne Darakta Janar na kwamitin kamfen neman tazarcen Akume a zaɓen gwamna a 2003.

Ƴa tattara kayansa ya bar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma ya koma jam'iyyar APC a ƙarshen makon nan da ya wuce.

Ya riƙe manyan muƙamai daban-daban da suka haɗa da mataimakin shugaban jami'a, ƙaramin ministan makami da ƙarafa da lafiya har sau biyu.

Kara karanta wannan

Babban jigo kuma mamban kwamitin amintattun PDP ya sauya sheƙa zuwa APC

Sannan kuma ya riƙe muƙamin jadakan Najeriya a ƙasar Mexico da kuma ambasada a ƙasar Kanada.

Meyasa Hagher ya koma APC

"Na samu natsuwa yanzu, na shigo APC ne ba don hangen muƙami ba sai don na taimaka wajen gina jam'iyyar kuma na taimaki abokina, George Akume, ɗan ƙabilar Tiv na farko da aka naɗa SGF."
"Akume ne jagoran APC a Benuwai, mafi yawan al'ummata APC suka zaɓa shiyas ana ga ya kamata na taho mu haɗe da su."

- Farfesa Hagher.

Atiku ya karɓi bakuncin Obi

A wani rahoton mun kawo maku cewa Manyan ƴan takarar shugaban ƙasa a 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun gana yayin da ake shirin zaɓen 2027

Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce abin alfahari da girma ne da ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Anambra, Obi.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel