PDP Ta Sake Samun Nakasu Bayan Tsohon Kakakin Majalisa Ya Fice Daga Jam'iyyar

PDP Ta Sake Samun Nakasu Bayan Tsohon Kakakin Majalisa Ya Fice Daga Jam'iyyar

  • Jam'iyyar PDP ta samu sabon naƙasu a jihar Edo bayan ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar
  • Francis Okoye wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar ne ya yi murabus daga PDP a cikin wata wasiƙa da ya aika ga shugaban jam'iyyar na mazaɓarsa
  • Ya bayyana cewa daga cikin dalilansa na barin PDP akwai yadda gwamnatin Gwamna Obaseki ta mayar mutanen yankinsa saniyar ware

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Francis Okiye, ya fice daga jam’iyyar People Democratic Party (PDP).

Francis Okiye, wanda tsohon ɗan takarar gwamna ne a jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar ne a watan Oktoban 2020 bayan da shi da wasu sun fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi jimami da ɗan majalisar tarayya, Dogonyaro ya rasu a Abuja

Jigon PDP ya fice daga jam'iyyar
PDP ta rasa babban jigo a jihar Edo bayan ya fice daga jam'iyyar Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa ya aika da wasiƙar murabus ɗinsa ga shugaban jam'iyyar PDP na mazaɓa ta uku, Arue, Uromi a ƙaramar hukumar Esan ta Arewa ta Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Francis Okiye ya bar PDP?

A cikin wasiƙar ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda yadda aka mayar da mutanen yankinsa da magoya bayansa saniyar ware a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Godwin Obaseki, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:

"Na yi murabus daga zama mamban jam'iyyar PDP daga ranar 10 ga watan Mayun 2024. Na sanar da hakan ga jam'iyyar PDP ta hannun shugabanta na mazaɓa ta."
"Dalilin yanke wannan hukuncin ya biyo bayan mayar da mafi yawan mutanen yankina da magoya bayana saniyar ware da gwamnatin jiha ƙarƙashin Gwamna Godwin Obaseki ta yi daga shirye-shirye jam'iyya da na gwamnati."

Kara karanta wannan

Ganduje da APC sun yi rashi, dubunnan mambobin jam'iyyar sun koma NNPP

"Bugu da ƙari kuma, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ya ce zai ɗora daga inda gwamnan ya tsaya idan ya lashe zaɓen watan Satumba. Sauran dalilan barin jam'iyyar kuma na ƙashin kaina ne."

Sai dai, tsohon kakakin majalisar bai bayyana inda jirgin siyasarsa zai sauka ba a nan gaba.

Tsohon gwamna ya fice daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya koma jam'iyyar APC.

Ibrahim Shehu Shema ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu bayan ya watsar da jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng