Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Shirin Kafa Jam'iyya Domin Lallasa Tinubu a 2027
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Pat Utomi ya jaddada cewa yana nan kan aikin kafa sabuwar jam'iyya gabanin zaɓen 2027
- Utomi ya bayyana cewa jam'iyyu da ƴan siyasar da ake da su yanzu a Najeriya ba za su iya ceto ƙasar daga halin da take ciki ba
- Ya ce a makon nan zai yi taro a Legas, sannan zai ƙara yin wani taron a Abuja a makon gobe duk kan sabuwar jam'iyyar da za su kirkiro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Pat Utomi, fitaccen masanin tattalin arziki kuma ɗan siyasa ya jaddada cewa yana nan kan bakarsa na kafa sabuwar jam'iyar siyasa gabanin zaɓen 2027.
Mista Utomi ya bayyana haka ne yayin zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) jim kaɗan bayan da yawo Najeriya daga Amurka ranar Alhamis.
Ya ce jam'iyyar APC mai mulki da sauran jam'iyyun adawa da ake da su yanzu ba za su iya ceto ƙasar nan ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, jam’iyyun siyasar da ake da su a halin yanzu sun gaza cika muradun jama’a kuma ba su taɓuka komai wajen gina kasa.
Utomi ya faɗi manufar kafa sabuwar jam'iyya
Pat Utomi ya ƙara da cewa sabuwar jam'iyyar da suke shirin kirkiro wa za ta ƙalubalanci tsarin siyasar da ake tafiya a kai yanzu da kuma samar da shugabanci na gari.
"Wannan shi ne dalilin da yasa na dawo Najeriya jiya don ci gaba da wannan aiki (kafa babbar jam'iyyar). Na yi imani tsarin jam'iyyun da muke da su yanzu ya gaza gaba ɗaya.
"Jam'iyyun siyasa sun sauka daga tafarkin demokuraɗiyya kuma ba su da wata manufa. A fili yake yanzu jam'iyyu da ƴan siyaar nan ba za su iya ceto Najeriya ba.
"A tsarin da muke tafiya a kai yanzu, ko mutanen kirki idan suka shiga waɗannan jam'iyyun za a rinjaye su, su koma ƴan son rai."
- Pat Utomi.
Utomi ya fara tarruka a Legas, Abuja
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar ADC ya ce don haka ya zama wajibi a haifo sabon tsarin siyasa wanda zai tsamo Najeriya daga rami, cewar rahoton Vanguard.
Utomi ya ce a kokarin kirkiro sabuwar jam'iyyar zai gudanar da taro a Legas a wannan makon kuma zai yi wani taron a Abuja a makon gobe kafin ya kira taron manema labarai.
Jimoh Ibrahim ya bukaci a kori ministoci
A wani rahoton na daban Sanata Jimoh Ibrahim ya shawarci Bola Ahmed Tinubu ya tashi tsaye, ya sallami wasu daga cikin ministocinsa saboda ba zasu iya ba.
Ibrahim, mamban kwamitin kasafi na majalisar dattawa ya koka cewa Tinubu ya ɗauko wasu mutane da ake zargi da cin hanci ya ɗora a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng