EFCC: Yahaya Bello Ya Yi Shigar Mata Domin Ya Tsere Daga Najeriya? Gaskiya Ta Fito
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bai sanya tufafin mata domin ya yi basaja ya gudu daga Najeriya da kaucewa yunƙurin kama shi ba
- Bincike ya nuna hoton da ake yaɗawa da sunan Yahaya Bello ne ya yi shigar mata bayan EFCC ta fara nemansa ruwa a jallo ba na gaskiya ba ne
- Bayan gudanar da binciken gano asalin hoto na Google, an fahimci hoton da aka jirkita na marigayiyar matar Sanata Ken Nnamani ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta musamman a manhajar Whatsapp cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi yunƙurin tserewa daga Najeriya ba gaskiya bane.
Tun farko dai an fara yaɗa wani hoto da ake zargin cewa tsohon gwamnan ne ya yi shigar mata domin ya samu damar barin Najeriya kuma ya gujewa hukumar EFCC.
Idan ba ku manta ba, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa da jallo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma a wani rahoto, Dubawa ta gudanar bincike domin gano gaskiyar hoton da aka ce Yahaya Bello ne ya yi shigar ƴan daudu zai gudu ya kaucewa EFCC.
Da gaske Yahaya Bello ya sa kayan mata?
Yayin da aka gudanar da binciken gano asalin hoto a manhajar 'Google Reverse' an gano cewa hoton da ake yaɗawa ba Yahaya Bello bane.
Binciken ya nuna cewa hoton na marigayya matar Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattawa, Jane Nnamani ne aka ɗauko aka jirkita shi.
Haka nan kuma an tattaro cewa hoton dai shi ne aka yi amfani da shi wajen sanar da rasuwar Jane Nnamani a shekarar 2023.
Yahaya Bello ya gudu daga Najeriya?
Daga ƙarshe an karƙare binciken da cewa hoton da aka yi amfani da sunan Yahaya Bello ya sa kayan mata zai gudu na tsohuwar matar Nnamani ne aka jirkita.
EFCC na ci gaba da ƙoƙarin gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi kan tuhume-tuhume 19 da suka ƙunshi halasta kuɗin haram, cin amana da satar N80bn.
EFCC ta kai samame kasuwar canji
A wani rahoton na daban, jami'an hukumar EFCC sun waiwayi ƴan canji a kasuwar bayan fage da ke Wuse a birnin tarayya Abuja ranar Talata.
Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar ya tabbatar da cewa jami'an EFCC sun kama wasu mutane yayin da suka kai samame a kasuwar.
Asali: Legit.ng