"Da Yawa Ba Su da Muƙamai": Jigon APC Ya Magantu Kan Zargin Rikicin Tinubu da El Rufai
- Kwamred Podar Johnson, jigon APC a jihar Plateau ya magantu kan zargin rikici tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Nasir El-Rufai
- Johnson ya ce babu wata alaka mai tsami tsakanin Tinubu da tsohon gwamnan Kaduna a yanzu kamar yadda ake yaɗawa
- Sai dai ya bukaci Tinubu ya rinka tabbatar da adalci yayin nade-nade inda ya ce da yawa sun bautu a APC amma suna zaune
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Jigon jam'iyyar APC a jihar Plateau, Podar Yiljwan Johnson ya magantu kan alakar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Nasir El-Rufai.
Johnson ya ce babu wata matsala tsakanin Tinubu da Nasir El-Rufai kamar yadda ake zargi a wasu ɓangarori.
Mene gaskiya kan alakar El-Rufai da Tinubu?
Jigon na APC ya ce batun cewa akwai wani rikici ko rashin jituwa tsakanin mutanen biyu kwata-kwata ba gaskiya ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamred Podar ya bayyana haka ne yayin hira da Legit a ranar Lahadi 5 ga watan Mayun 2024.
Jigon APC ya shawarci Tinubu kan muƙamai
Tsohon dan takarar jam'iyyar har ila yau ya bukaci Tinubu ya rika adalci yayin nadin mukamai a kasar.
"Ban san wani rashin jituwa tsakanin Tinubu da El-Rufai ba, mulki daga Allah ya ke."
"Wasu da dama sun bautu a APC Amma ba su da mukami, gamu nan mun sha wahala a jam'iyyar amma har yanzu babu abin da aka bamu."
"Tinubu ya nada wadanda da ya ke ganin za su inganta Najeriya, kawai abin da muke so shi ne yin adalci a nade-nade, ya kawo mutane daga dukkan bangarorin kasar."
"Ya kamata Tinubu ya dawo da shugaban jam'iyyar APC Arewa ta Tsakiya saboda tabbatar da adalci a jam'iyyar."
- Podar Johnson
Jigon PDP ya zargi Tinubu kan El-Rufai
A wani labarin, kun ji cewa jigon jami'yyar PDP, Segun Showunmi ya ce Shugaba Tinubu ya ci amanar kan yadda Nasir El-Rufai da Yahaya Bello.
Showunmi ya nuna damuwa musamman kan yadda shugaban kasar ya yaudari tsofaffin gwamnonin duk da wahalar da suka sha masa.
Wannan na zuwa ne bayan goyon baya da tsofaffin gwamnonin suka ba Bola Tinubu a zaben da aka gudanar.
Asali: Legit.ng