Ana Daf da Gudanar da Zabe, APC da PDP Sun Yi Barin 'Yan takarar Gwamna

Ana Daf da Gudanar da Zabe, APC da PDP Sun Yi Barin 'Yan takarar Gwamna

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, dukkan jam'iyyun APC da PDP a jihar sun yi rashin jiga-jigai
  • 'Yan takarar jam'iyyar APC da PDP a zaben gwamnan jihar guda biyu sun yi murabus daga jamiyyunsu kan wasu dalilai
  • Dakta Felix Akhabue na jam'iyyar PDP da kuma 'yar takarar APC, Dakta Victoria Amu sun yi watsi da jam'iyyunsu bayan zaben fidda gwani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Jam'iyyun APC da PDP sun tafka babban rashi a jihar Edo yayin da 'yan takarar gwamna suka yi murabus.

Dan takarar gwamnan jihar a PDP, Dakta Felix Akhabue ya watsar da jam'iyyar bayan gudanar da zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

"Zai yi wahala": Lauyan APC ya fadi hanya 1 da Ganduje zai rasa muƙaminsa a jam'iyya

Jam'iyyun PDP da APC sun rafka babban rashin jiga-jigansu bayan zaben fidda gwani
'Yan takarar gwamna a zaben jihar Edo na jam'iyyar PDP da APC sun yi murabus. Horo: Peoples Democratic Party, All Progressives Congress.
Asali: Facebook

Rashin da APC, PDP suka yi a Edo

Har ila yau, 'yar takarar gwamnan a jam'iyya APC, Dakta Victoria Amu ita ma ta yi murabus daga jam'iyyar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a karshen wannan shekara da muke ciki.

A bangarensa, Dakta Akhabue ya ce ga yi murabus din ne saboda tsantsan rashin adalci a jami'yyar, cewar rahoton Vanguard

Tsohon dan takarar ya bayyana haka ga shugaban jam'iyyar a mazaba ta 7 da ke karamar hukumar Esan ta Yamma a cikin wata takarda.

"Na rubuta wannan takarda domin tabbatar maka cewa na yi murabus daga ci gaba da kasancewa mamban jam'iyyar PDP."
"Na dauki wannan mataki ne ganin yadda ake gudanar da abubuwa ba bisa adalci da kuma tsari ba."

Kara karanta wannan

"Ni ne sila": Tsohon gwamna da ya fice a PDP ya magantu bayan jiga-jiganta sun watse

- Felix Akhabue

Musabbabin murabus din 'yar takarar APC

Dakta Amu a bangarenta, ta ce ta yi murabus din ne saboda wasu dalilai na karan kanta da kuma iyalanta.

"Ina godiya da dama da aka bani a matsayin hadima a gwamnatin Adams Oshiomole har na tsawon shekaru bakwai."
"Ina kuma kara godiya kan muƙamin da Gwamna Godwin Obaseki ya bani na hadima a gwamnatinsa har na tsawon shekara daya."
"Na godewa magoya bayana yayin da na nemi takarar majalisar jiha a 2022 da kuma takarar kujerar gwamna a zaben 2024."

- Victoria Amu

Lauyan APC ya magantu kan Ganduje

Kun ji cewa lauyan APC, Abdulkarim Kana ya yi fashin baki kan dambarwar shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje.

Kana ya ce a yanzu babu wanda ke da ikon dakatar da Ganduje daga mukaminsa yayin da ake bincike sai kwamitin NWC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.