Tsagin NNPP Ya Kai Karar Kwankwaso da Wasu Mutum 13 Gaban EFCC, bayanai sun fito

Tsagin NNPP Ya Kai Karar Kwankwaso da Wasu Mutum 13 Gaban EFCC, bayanai sun fito

  • Tsagin jam'iyyar NNPP ya kai ƙarar Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a gaban hukumar EFCC
  • Tsagin ya shigar da ƙarar ne bisa zargin Ƙwankwaso da wasu mutum 13 sun yi sama da faɗi da kuɗaɗen jam'iyyar waɗanda sun kai N2.5bn
  • A cikin ƙarar sun buƙaci hukumar yaƙi da cin hancin da ta binciki asusun jam'iyyar tun daga watan Maris na 2022 har zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani tsagin jam'iyyar NNPP ya kai ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso, da wasu mutane 13 a hukumar EFCC.

Tsagin na NNPP ya kai ƙarar Kwankwaso gaban hukumar yaƙi da cin hancin ne bisa zargin karkatar da sama da N2bn.

Kara karanta wannan

Binciken Matawalle: An yi sabuwar fallasa kan masu zanga-zanga a EFCC

An kai karar Kwankwaso gaban EFCC
Tsagin NNPP ya kai karar Kwankwaso gaban EFCC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Wane zargi ake yi wa Kwankwaso?

Tsagin na NNPP a cikin ƙarar wacce sakatarenta na ƙasa, Oginni Olaposi, ya shigar ya yi zargin cewa an sama da faɗi da kuɗaɗen asusun jam'iyyar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oginni Olaposi a cikin ƙarar wacce ya aike ga shugaban EFCC, ya ce kusan aƙalla N2.5bn da aka samu daga siyar da fom na takara da kuɗaɗen gudunmawa, shugabannin jam'iyyar da aka kora ba su ba da bayani a kansu ba.

Sakataren ya koka da cewa sama da faɗi da kuɗaɗen ya sanya ba a biya kuɗaɗen alawus na wakilan jam'iyyar ba da suka yi aiki a zaɓen 2023 a faɗin ƙasar nan.

Ya buƙaci hukumar EFCC da ta binciki asusun jam'iyyar NNPP tun daga watan Maris na 2022 har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Matawalle: EFCC ta yi magana kan binciken tsohon gwamnan Zamfara

Wane martani Kwankwaso ya yi?

Da yake mayar da martani, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Kwankwaso, Ladipo Johnson, ya ce jam'iyyar ba ta da wani tsagi, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ladipo ya haƙiƙance cewa wanda ba ɗan jam'iyya ba, ba shi da hurumin tambayar yadda aka kashe kuɗaɗen jam'iyyar.

Yayin da yake bayyana tsagin a matsayin masu son kawo ruɗani, Ladipo ya ce jam'iyyar ba ta damu ba kan koken da aka rubuta a kan Kwankwaso bisa zargin yin sama da faɗi da kuɗaɗen.

Tsagin NNPP ya dakatar da Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin amintattu na wani tsagi na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Tsagin na NNPP ya dakatar da gwamnan ne har na tsawon watanni shida bisa zarginsa da hannu a ayyukan da suka saɓawa jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng