Mataimakin Gwamna da Aka Tsige Ya Ki Maido Motocin Gwamnati Duk da Barin Ofis

Mataimakin Gwamna da Aka Tsige Ya Ki Maido Motocin Gwamnati Duk da Barin Ofis

  • Philip Shaibu bai da niyyar dawo da motocin ofis duk da majalisar dokokin jihar Edo ta tsige shi daga kan karaga
  • Tsohon mataimakin gwamnan na Edo ya kare kan shi bayan ya rike motocin da aka warewa ofishinsa da yake mulki
  • Kwamred Philip Shaibu ya kafa hujja da cewa shi ya yi amfani da kudin aljihunsa wajen gyara tsofaffin motocin nan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Edo - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya yi magana a game da halin da yake ciki bayan an tunbuke shi kwanaki.

Kwamred Philip Shaibu ya tabo zancen mulkin Edo, siyasar ubangida da kuma motocin da aka ba shi a lokacin yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Digiri dan Kwatano: Gwamnatin tarayya ta juyo kan masu takardun bogi a Najeriya

Philip Shaibu
Tsohon mataimakin Gwamna a Edo, Philip Shaibu Hoto: @HonPhilipShaibu
Asali: Twitter

Philip Shaibu da motocin mataimakin gwamna

A tattaunawarsa da Punch, ‘dan siyasar ya zurfafa magana a game da motocin da aka mallaka masa a yayin da ake kamfe a Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wajen wannan hirar ne Kwamred Philip Shaibu ya bayyana cewa ba zai dawo da wadannan motoci ba duk da ya bar ofis.

Tsohon mataimakin gwamnan wanda majalisar dokoki ta tsige ya ce masu neman ya maidowa gwamnati motocin ba su da tausayi.

Philip Shaibu ya yi gaba da motocin gwamnati

"Motocin da ake magana Prado SUV biyu ne, Hilux daya sai wata Land Cruiser."
"Na dauke duka motocin nan…saboda haka, za ku iya ganin irin rashin tausayin ‘dan adam."

- Philip Shaibu

Tsohon mataimakin gwamna ya yi raddi

Shaibu yake cewa motocin nan da ake magana a kai ba sababbi ba ne, a cewarsa tsofaffin ne da aka gyara, aka mallakawa ofishinsa.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

Nairaland ta kawo labarin, ta ce ‘dan siyasar ya yi ikirarin shi ya dauki motocin zuwa wurin gyara, ya kashe masu kudi daga aljihunsa.

Kamar yadda ya fada, Lucky Imasuen da mai dakin Dr. Pius Odubu sun yi amfani da motocin, kafin a ba shi da yake kan mulki a Edo.

"Na dauki motocin nan zuwa wurin makaniki, shi ya canza injinsu, kuma ya gyara su. Wadannan su ne motocin da ake fada mani in dawo da su."
"Mota guda kurum na samu a tsawon shekaru kusan takwas da na yi a matsayin mataimakin gwamnan jihar."

- Philip Shaibu

Gwamnoni da suka sauya-sheka a tarihi

A baya mun kawo rahoto dauke da jerin gwamnonin jihohin da suka canza jam'iyya bayan sun dare mulki daga zaben 1999 zuwa yau.

Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi sun taba barin PDP, Abdulfatah Ahmad ne gwamna da ya sauya-sheka sau biyu a mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng