"Ya Kware a Cin Amana": APC Ta Ja Kunnen Tinubu Kan Sake Jiki da Gwamnan PDP
- Jiga-jigan jam'iyyar APC a Bayelsa sun ja kunnen Bola Tinubu kan sakewa da Mai girma Gwamna Douye Diri na jihar
- Masu ruwa da tsakin sun gargadi Tinubu da ya yi hankali da gwamnan wanda suka ce ya kware a fannin cin amana da iya munafurci
- Wannan na zuwa ne bayan zargin gwamnan wanda ɗan PDP ne yana ɗasawa da wasu mukarraban shugaban inda hakan ke saka shakku
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC a jihar Bayelsa sun gargadi Shugaba Bola Tinubu.
Jam'iyyar ta tura gargadin ne kan shisshigi da Gwamna Diri Douye ya ke yi ga Tinubu inda ta ce ya yi hankali.
Abin da APC ta ce kan Gwamna Diri
Jiga-jigan APC suka ce Diri cikakken maci amana ne wanda bai kamata a yi saurin amincewa da shi ba inda suka ce ba shi da tasiri a siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Cif Samuel Yousuo ya tura ga Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Samuel ya ce Gwamna Diri ya kware wurin cin amana da siyasar hadama inda suka ce ba za su jure irin halayensa ba.
Punch ta bankado cewa akwai alaka ta musamman tsakanin Gwamna Diri wanda cikakken dan PDP ne da kuma mukarraban Tinubu.
Har ila yau, jiga-jigan jami'yyar sun bayyana Diri a matsayin maras amfani a siyasa wanda ba zai tsinanawa APC komai ba, cewar Sahara Reporters.
APC ta gargadi Tinubu kan Gwamna Diri
"Muna amfani da wannan daman domin sanar da kai cewa Diri kwata-kwata ba abin yarda ba ne.
"Diri ya guji dukkan shugabannin PDP a jiharsa, muna tabbatar maka cewa ba shi da wani tasiri a siyasance, zai shigo APC ne ya zama mana jangwangwan."
- Samuel Yousuo
Shema ya dawo jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya dawo jam'iyyar APC mai mulki.
Shema ya watsar da jam'iyyar PDP ne a jiya Alhamis 2 ga watan Mayu a gundumar Shema da ke karamar hukumar Dutsin-Ma.
Asali: Legit.ng