Jigon PDP ya 'Fallasa' Babban Dalilin Rikicin Nyesom Wike da Sabon Gwamnan Ribas
- Dele Momodu, jigo a babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya bayyana dalilan barakar da aka samu tsakanin tsohon gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da Siminalayi Fubara
- Ya bayyana cewa rigimar ta kunno kai ne kan wanda zai yi iko da baitul malin jihar wacce ya yi zargin shugaba Bola Tinubu na son ya yi iko da shi
- Dele Momodu ya ce jam'iyya mai mulki ta APC na amfani da Nyesom Wike wajen kawo baraka a PDP, amma za su shawo kan matsalar sannu a hankali
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Rivers-Wani jigo a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya bayyana dalilin barakar da ke tsakanin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da magajinsa Siminalayi Fubara.
A cewar Momodu, shugabannin biyu sun samu sabani kan wanda zai rika juya asusun gwamnatin Ribas ne.
Tinubu yana amfani da Wike a PDP?
A hirar da ya yi da Channels Television, Dele Momodu ya ce Wike da Fubara sun fara takun saka ne tun bayan da Fubara ya dare kan mulkin jihar tare da tafiyar da al'amuransa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kokarin amfani da Wike wajen shiga baitul malin jihar Ribas din.
Dele Momodu ya kara da cewa kudin jihar Ribas na taka muhimmiyar rawa wajen zaben kasar nan, shi ya sa Shugaba Tinubu ke son Wike ya rike musu jihar.
"Za mu yi sulhu a PDP," Dele Momodu
Daya daga cikin jiga-jigai a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya ce su na sane da yadda APC karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke amfani da daya daga cikinsu wajen rarraba kan 'ya'yan jam'iyyar.
Dele Momodu wanda ya ce da mamaki yadda gwamnatin Tinubu ke kokarin murkushe adawa duk kuwa da yadda ya jagoranci adawa lokacin ya na gwamnan jihar Lagos, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Sai dai ya na ganin sannu a hankali za su dinke barakar, domin a cewarsa, Atiku Abubakar dan takararsu a zaben shugaban kasar da ya gabata na kokarin hada kawunan 'yan jam'iyyar.
Dele Momodu ya ce za su ba APC mamaki a zabe mai zuwa na shekarar 2027.
"Zan kare jihar Rias," Fubara
A baya mun kawo muku cewa gwamnan jihar Ribas, Fubara Siminalayi ya sha alwashin gudanar da al'amuran jiharsa ba tare da durkusawa wani ba.
Gwamnan ya kuma sha alwashin aiki tukuru wajen kare albarkatun jiharsa a dai-dai lokacin da su ke tsaka da dambarwa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng