El-Rufai: PDP Ta Sake Bankaɗo Aiki, Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Kuma Shiga Matsala

El-Rufai: PDP Ta Sake Bankaɗo Aiki, Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Kuma Shiga Matsala

  • Yayin da ake bikin ranar ma'aikata a Najeriya, jam'iyyar PDP ta sake bukatar binciken Nasir El-Rufai a Kaduna
  • Jam'iyyar ta bukaci kwamitin binciken El-Rufai ya zurfafa har kan zargin korar ma'aikata 27,000 da tsohon gwamnan ya yi
  • PDP ta zargi El-Rufai da korar ma'aikatan ba bisa ka'ida ba kuma da rashin biyansu hakkokinsu bayan sallamarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Jami'yyar PDP a jihar Kaduna ta bukaci a binciki tsohon gwamna, Nasir El-Rufai Kan korar ma'aikata.

Jami'iyyar PDP ta bukaci kwamitin binciken da Majalisar jihar ta kafa ya yi bincike kan korar ma'aikata 27,000 da El-Rufai ya yi ba tare da biyansu hakkokinsu ba.

Kara karanta wannan

'Ba zai tsinana komai ba', gamayyar 'yan siyasa sun soki Tinubu a ranar ma'aikata

PDP ta bukaci sake bincikar El-Rufai kan korar ma'aikata
Jami'iyyar PDP ta bukaci kwamitin bincike ya sake duba kan korar ma'aikata da Nasir El-Rufai ya yi. Hoto: @elrufai.
Asali: Twitter

Bukatar PDP kan binciken El-Rufai a Kaduna

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jami'yyar a jihar, Abraham Alberah Catoh ya fitar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abraham Alberah Catoh ya ce wannan aika-aika na tsohon gwamnan ya saba doka kuma cin zarafin aikin gwamnati ne.

PDP ta bukaci hakan ne yayin bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a yau Laraba 1 ga watan Mayu, Daily Post ta tattaro.

PDP ta zargi El-Rufai da korar ma'aikata

"Muna kira ga kwamitin binciken da Majalisar jihar Kaduna ta kafa ta binciki yadda gwamnatin El-Rufai ta gudanar da mulki."
"Ya kamata ta fadada bincikenta har kan korar ma'aikata 27,000 da ya yi ba bisa ka'ida ba kuma ba tare da biyansu hakkokinsu ba."
"Jam'iyya PDP ta himmatu wurin tabbatar da inganta kasa tare da goyon bayan gwamnati domin inganta walwalar ma'aikata."

Kara karanta wannan

"Ka ci amanarsu": Jigon PDP ya dira kan Tinubu game da El-Rufai da Yahaya Bello, ya fadi dalilai

- Abraham Catoh

Jam'iyyar ta ce ma'aikata na gwamnati da na ma'aikatu masu zaman kansu su ne suke kawo ci gaba a fannin tattalin arziki.

A karshe, PDP mai hamayya a kasa da jihar ta taya dukkan ma'aikata murnan zagayowar wannan rana ta su a yau 1 ga watan Mayu.

Majalisa ta fara bincike kan El-Rufai

A wani labarin, an ji cewa kwamitin da Majalisar jihar Kaduna ta kafa kan binciken Nasir El-Rufai ya fara aiki kan badakalar da ake zargi.

An kafa kwamitin ne domin binciken tsohuwar gwamnatin El-Rufai bayan zargin Gwamna Uba Sani kan ya bar masa tulin bashi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.