Kungiya Ta Nesanta Kanta Daga Zanga Zangar Neman Tsige Ganduje, Ta Yi Fallasa
- Wata ƙungiya ta fito fili ta nesanta kanta daga zanga-zangar da wasu mambobinta suka yi domin neman Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus
- Ƙungiyar ta bayyana cewa masu zanga-zangar korarrun mambobinta ne da aka sallame su saboda aikata laifuka
- A sanarwar da babban sakataren ƙungiyar ya fitar ya yi nuni da cewa kuɗi aka ba su domin gudanar da zanga-zangar neman murabus ɗin Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wata ƙungiya mai suna 'Concerned North Central APC Stakeholders', ta nesanta kanta daga zanga-zangar neman Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa na shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Ƙungiyar ta buƙaci masu zanga-zangar da su mayar da kuɗaɗen da suka karɓa domin gudanar da zanga-zangar.
Hakan dai na ƙunshe a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren ƙungiyar, Malam Shehu Ibrahim tare da shugabanta na ƙasa, Kwamared Aodona Patrick, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wa ke da hannu a zanga-zangar?
Ƙungiyar ta ce waɗanda suka yi zanga-zangar ƴaƴanta ne da aka kora, waɗanda a yanzu suka samu wata sabuwar sana’a ta ɓata sunan ƴan Najeriya masu ƙima domin samun abin duniya, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa babban burinsu shi ne a tsige Ganduje daga muƙaminsa bisa umurnin Shugaba Bola Tinubu.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Muna so mu bayyana a fili cewa masu zanga-zangar neman murabus ɗin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ba mambobinmu ba ne."
"Korarrun mambobi ne da aka kore su saboda aikata laifuka. Ba mu yi mamakin ganin sun ɗauki wannan sheɗaniyar hanyar ba."
"A ƴan kwanakin nan, suna ɓata sunan ƴan Najeriya masu ƙima domin samun kuɗaɗe, kwanan nan aka ba su kwangilar ɓata sunan Ganduje."
Batun dakatar da Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ce ke da hannu a dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar.
Tsohon gwamnan na jihsr Kano ya ce ko kaɗan bai damu da dakatarwar da aka yi masa ba wacce ya zargi gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kitsawa.
Asali: Legit.ng