Ondo 2024: Jam’iyyar PDP Ta Tsayar da Dan Takarar Gwamna da Zai Kara da Aiyedatiwa
- Jam'iyyar PDP ta tsayar da Ajayi Agboola a matsayin dan takararta a zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar a watan Nuwamba 2024
- Agboola ya samu rinjaye kan abokan karawarsa bayan ya samu kuri'u 264 yayin da mai binsa Hon. Kolade Akinjo ke da kuri'u 157
- Akalla daliget 621 da suka fito daga kananan hukumomi 18 na jihar ne suka kada kuri'a a zaben fidda gwanin da aka yi yau Alhamis
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Ondo - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya zama dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan da za a yi a watan Nuwamba.
Ajayi ya rike mukamin mataimakin gwamna a mulkin marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu a wa'adinsa na farko daga 2016 zuwa 2020 kafin su raba gari.
A zaben fidda gwani da PDP ta gudanar a yau Alhamis, ya samu kuri’u 264, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuri'un da masu neman takara suka samu
Ya kayar da wasu ‘yan takarar da suka hada da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Kolade Akinjo wanda ke bin bayansa da kuri'u 157.
Haka kuma, tsohon kwamishinan muhalli, Cif Ebiseni Olusola, ya zo a na uku da kuri’u 99, yayin da Injiniya Adeolu Akinwumi ya samu kuri'u 64 inda ya zo na hudu.
Otunba Bamidele Akingboye ya samu kuri’u 24, yayin da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, John Ola Mafo ya samu kuri’u tara, sai kuma Bosun Arebuwa ya samu kuri’u biyu.
Jaridar Vanguard ta rahoto an fafata a zaben wanda wakilai akalla 621 daga kananan hukumomi 18 na jihar ne suka kada kuri'unsu.
Manyan masu neman takara 3 a PDP
Tun da fari, Legit Hausa ta kawo maku bayani dalla-dalla game da manyan masu neman takarar kujerar gwamnan jihar Ondo karkashin jam'iyyar PDP.
Daga cikin manyan masu neman takarar akwai Ajayi Agboola, Otunba Bamidele Akingboye (OBA) da Sola Ebiseni wadanda aka fi kyautatawa tsammani.
Asali: Legit.ng