Kano: Jigon APC Ya Fadi Hanya Mafi Sauƙi da Kwankwaso Zai Samu Shugabancin Najeriya
- Tsohon mataimakin shugaban APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi magana kan takarar Sanata Rabiu Kwankwaso
- Salihu ya ce zai yi wahala Kwankwaso ya samu abin da ya ke nema har sai idan APC ta ba shi dama domin gyara matsalolinsa
- Jagoran na APC ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jaridu inda ya ce matsalar Ganduje da Kwankwaso siyasa ce kawai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jigon jami'yyar APC, Salihu Lukman ya yi magana kan takarar shugabancin Sanata Rabiu Kwankwaso.
Lukman ya ce zai yi wahala Kwankwaso ya yi tasiri a jam'iyyar NNPP kan muradinsa na neman shugabancin Najeriya.
Yadda APC za ta ba Kwankwaso dama
Jigon APC ya bayyana haka ne a yau Laraba 24 ga watan Afrilu yayin hira da gidan talabijin na Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce jam'iyyar APC za ta iya taimaka masa wurin bude masa kofa domin ya shigo tare da gyara matsalolinsa a ƙasar.
Har ila yau, Lukman ya ce za a iya dakile matsalar Ganduje da Kwankwaso tun farko wanda jam'iyyar ta yi sakaci har Sanatan ya watsar da APC.
"Ya kamata mu tura Ganduje domin sake gyara komaɗar da aka samu tun da siyasa ce ta jawo, ta haka ne kawai za a gyara matsalar."
- Salihu Lukman
Jigon APC ya shawarci sasantawa da Kwankwaso
"Babban burin Kwankwaso shi ne ya zama shugaban ƙasa, a ina yanzu wannan buri nasa zai cika."
"Hakan zai daukeshi shekaru wurin tattaunawa da jama'a a ɓangarorin kasar wanda zai ya wuce lokacinsa."
"Za mu iya taimaka masa wurin ba shi dama ya shigo APC tare da sasanta shi da Ganduje a siyasance."
- Salihu Lukman
"APC ce mafita ga 'yan Najeriya" - Ganduje
Kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yi albishir ga 'yan Najeriya kan mulkin Bola Tinubu.
Abdullahi Ganduje ya ce jam'iyyar APC ita ce kadai za ta dakile matsalolin kasar a halin da ta ke ciki a cikin sauki.
Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka a Gombe yayin mika tutocin jam'iyyar ga 'yan takarar shugabancin kananan hukumomi.
Asali: Legit.ng