Mambobin NNPP Sun Buƙaci Gwamna Yusuf Na Kano Ya Yi Murabus Cikin Sa'o'i 48, Ta Faɗi Dalili
- Wasu mambobin jam'iyyar NNPP a jihohin Arewa 19 sun bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi murabus
- Tawagar masu ruwa da tsakin NNPP karkashin jagorancin Attahiru Musa da sakatarensa, Simeon Pam, sun kaɗa kuri'ar rashin amincewa da gwamnan
- Sun koka cewa Gwamna Yusuf bai fara wani aikin ci gaba da zai nuna tabbas zai yi wa al'ummar Kano shugabanci na gari ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wasu daga cikin mambobin jam'iyyar New Nigerian People Party watau NNPP sun buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gaggauta yin murabus.
Mambobin NNPP waɗanda suka fito daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun ba Gwamna Yusuf wa'adin awanni 48 ya sauka daga kujerar gwamna jihar Kano.
Meyasa NNPP ta nemi Abba ya sauka?
Masu ruwa da tsakin sun kaɗa kuri'ar rashin amincewa da gwamnan a wani taron gaggawa da suka kira ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da suka aiko wa Legit Hausa yau Litinin, 15 ga watan Afrilu, 2024.
Masu ruwa da tsakin dai sun tabbatar da cewa Gwamna Yusuf ya kaucewa manufar jam’iyyar kuma ya daina bin tafarkin tsare-tsaren ci gaban da NNPP ta zo da su domin ci gaban Kano.
Shugaban kungiyar, Honarabul Attahiru Musa da sakatarensa, Simeon Pam, sun ƙara da cewa Gwamna Yusuf ya fara amfani da dabarun shirme da farauta.
Sanarwar ta ce:
"A matsayinmu na masu ruwa da tsaki, ba za mu iya karewa mu nuna wani abu na tafiya daidai a fili ba amma a zahirin gaskiya babu abin da ke aiki.
"Ya kamata jihar Kano ta zama abin koyi ga Gwamnatin Tarayya.”
Masu ruwa da tsakin sun koka cewa ya kamata jihar Kano ta zama cibiyar samar da shugabanci nagari, wanda zai kalubalanci gwamnatin tarayya karkashin APC, amma abin sai ya juya.
Sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnan ya nuna ba shi da akida kuma NNPP ba ta nuna wani shiri na ci gaba da amfani da jihar a matsayin samfuri ba.
Gwamna Sule ya koka
A wani rahoton kuma Gwamna Abdullahi Sule ya koka kan yadda lamarin tsaro musamman yawaitar garkuwa da mutane a wasu sassan jihar Nasarawa.
Abdullahi Sule ya nuna damuwarsa ne yayin taron majalisar tsaron jihar da ya kira bayan ya dawo daga Umrah.
Asali: Legit.ng