Kano: 'Yaran' Kwankwaso Sun Shiga Gagarumar Matsala Kan Dakatar da Ganduje
- Ƙungiyar PFM ta zargi ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso da kulla maƙircin dakatar da shugaban APC
- Kungiyar wanda ke goyon bayan APC ta yi iƙirarin cewa Kwankwaso ne ya ɗauki nauyin shugabannin APC da suka dakatar da Ganduje
- PFM ta buƙaci mahukunta su gaggauta cafke masu hannu a kulla wannan makircin tare da gudanar da bincike kan wanda ya sa su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Wata ƙungiya da ake kira PFM a taƙaice ta yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta cafke waɗanda suka ƙulla makircin dakatar da Abdullahi Ganduje.
PFM ta bukaci jami'an tsaro su kama tare da bincikar waɗanda suka ɗauki nauyin dakatar da shugaban APC na ƙasa, Ganduje a gundumarsa da ke Kano.
Shugaban PFM, Emmanuel Aribigbe, ya yi zargin cewa duk da fuskokin mutanen da suka dakatar da Ganduje na cikin APC amma Rabiu Kwankwaso ne ya ɗauki nauyin su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso na da hannu a lamarin
Aribigbe ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aiko wa Legit Hausa ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu, 2024.
Shugaban ƙungiyar ya ce taron manema labarai da aka shirya a Kano aka sanar da ɗaukar mataki kan shugaban APC, mambobin NNPP ne suka jagorance shi.
PFM mai goyon bayan APC ta ce:
"Waɗannan mutanen magoya bayan Kwankwaso ne wanda kowa ya sani ba ya ƙaunar shugaban jam'iyyar mu. Muna kira ga jami'an tsaro su cafke mutanen da suka kira taron manema labaran kuma sun zaƙulo waɗanda suka turo su.
"Shugaban jam'iyyar mu na ƙasa bai aikata wani laifi da ya kai girman da za a iya dakatar da shi a gundumarsa ba."
"Don haka muna kira ga mambobi ɗa ɗaukacin al'umma musamman magoya bayan Ganduje da su kwantar da hankulansu kana su yi watsi da lamarin gaba ɗaya."
Bashir Ahmad ya tsoma baki
A wani rahoton kuma Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu kan dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga jam'iyyar APC
Bashir Ahmed ya ce idan har wannan dakatarwar ta tabbata to abin da ya faru da Adam Oshiohmole ne ke shirin faruwa da Ganduje.
Asali: Legit.ng