Shugabanci: An Faɗi Wanda Ya Cancanci Zama Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP Daga Arewa

Shugabanci: An Faɗi Wanda Ya Cancanci Zama Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP Daga Arewa

  • Wata kungiya a yankin Arewa ta tsakiya ta nuna goyon bayanta ga David Ombugadu ya zama shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa Ombugadu na da dukkan kwarewar da ake buƙata daga wanda zai gaji Iyorchia Ayu kuma ya farfaɗo da PDP
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu ƙusoshin jam'iyyar suka nemi a sauke muƙaddashin shugaban jam'iyyar, Ambasada Iliya Damagum

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Yayin da ake tsammanin Arewa ta Tsakiya ce za ta samar da shugaban APC na gaba, a halin yanzun an fara kawo waɗanda suka dace.

A wannan ƙaron, wata ƙungiya ta gabatar da ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawa a zaɓen 2023, David Ombugadu, domin ya shiga tseren jan ragamar PDP yayin da ake tunkarar 2027.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Ganduje ya bayyana abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi wa Tinubu

David Umbugadu.
Wata kungiyar ta nemi a bai wa Umbugadu damar jan ragamar PDP ta ƙasa Hoto: Nasarawa Mirror
Asali: Facebook

Kamar yadda Tribune Najeriya ta ruwaito rnaar 10 ga watan Afrilu, 2024, kwamitin zartasawa na jam'uyyar PDP ya shirya taro a makon gobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran a taron, NEC zai yanke shawara kan makomar Ambasada Iliya Damagum, wanda ga zama muƙaddashin shugaban PDP tun lokacin da Iyorchia Ayu ya rasa kujerar.

Yadda aka tsige Ayu daga PDP-NWC

Idan baku manta ba, babbar kotun jihar Benuwai mai zama a Makurɗi ce ta tsige Sanata Ayu daga muƙamin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa.

Ranar 2 ga watan Yuni, 2023, mai shari'a Maurice Ikpambese, ya yanke cewa Ayu ba mamban PDP bane, wanda hakan ya dakatar da shi daga komawa kujerar shugaban jam'iyya.

Ƙungiya ta gano wanda ya cancanci PDP

Amma a ranar Laraba wata kungiya mai suna, 'PDP Frontliners' ta bayyana cewa Ombugadu ne ya fi dacewa da jagorantar PDP yayin da ake kokarin farfaɗo da ita, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya bayyana muhimmin dalilin da ya sa ya sauya sheƙa zuwa PDP

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce wasu daga cikin masu ruwa da tsaki sun fara yawon neman shawarwari domin tabbatar da takarar David Umbugadu.

Shugaba, sakatare da kakakin ƙungiyar sun rattaba hannu kan sanarwar, inda ta ce:

"Idan ana son PDP ta dawo kan ganiyarta, to ya zama dole a kaucewa wasu ɓangarori da ke kokarin ƙwace iko da jam'iyyar, sannan a haɗa karfi wajen sake dabarun da zai ba PDP nasara a 2027."

PDP ta shiga sabuwar matsala

A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP ta sake shiga sabuwar matsala yayin da ƴan majalisar wakilan tarayya 60 suka yi barazanar ficewa daga cikin jam'iyyar.

Ƴan majalisun sun yi barazanar barin PDP ne matuƙar ba a sauya muƙaddashin shugaban jam'iyyar, Umar Damagum ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262