An Samu Sabani a NNPP Saboda Sabuwar Alamar Jam'iyyar da Kwankwaso ya Kaddamar

An Samu Sabani a NNPP Saboda Sabuwar Alamar Jam'iyyar da Kwankwaso ya Kaddamar

  • Wasu 'yan jam'iyyar NNPP sun yi watsi da sauya tambarin jam'iyyar daga alamar kayan marmari zuwa na ilimi duk da dadewar da su ka yi suna amfani da shi
  • Sun ce ba su ga dalilin da za a sauya alamar kayan marmarin da suka shafe shekaru 20 suna amfani da shi ba tare da an tuntube su ba, don haka ba za su lamuci sauyin ba
  • A 'yan kwanakin nan ne jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa sabuwar alamar na nuna yaki da talauci da kuma samar da ci gaban ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kara karanta wannan

Sauyin yanayi: Tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 za su samu aiki da gwamnatin tarayya

Kudu maso yamma- Jamiyyar NNPP dake Kudu maso yamma ta yi watsi da sauya alamar jam'iyyar daga kayan marmari zuwa tambarin ilimi bayan shafe shekaru 20 suna amfani da kayan marmarin.

Jam'iyyar NNPP ta fada rikici saboda sauya alamar kayan marmari
Tsagin jam'iyyar NNPP na ganin babu dalilin sauya alamar zuwa nau'in Kwankwasiyya Hoto:@officialNNPPng
Asali: Twitter

A wata sanarwa da tsagin jam'iyyar ya fitar dauke da sa hannun jamiin hulda da jama'arta, Kilamuwaye Badmus ya ce ba za su amince da sauya tambarin jamiyyar ba kamar yadda tribune ta ruwaito.

"Sauya tambarin bai zo gare mu ba a hukumance, saboda haka ba zai yiwu ba," a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Kilamuwaye Badmus.

'Dan siyasar ya shawarci gwamnan Kano da sauran zababbun 'yan siyasar da su ka samu nasara karkashin jam'iyyar da musu mara masu baya wajen ci gaba da amfani da alamar kayan marmari na jamiyyar,

Badmus ya kara da cewa:

"Menene dalilin sauya alamar jamiyyar zuwa kalar kwankwasiyya na ja da fari da ja ba tare da neman sahalewar 'yan jamiyyar ba"

Kara karanta wannan

"Za mu waiwayi bidiyon dala": Abba ya magantu kan shekara 8 na mulkin Ganduje a Kano

NNPP ta sauya alamarta a Najeriya

Jamiyyar NNPP yayin gudanar da babban taron jamiyyar a Abuja ta bayyana sabuwar alamar jamiyyar.

Leadership ta nuwaito cewa jigo a jamiyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jaddada muhimmancin, sabuwar alamar jamiyyar.

Kwankwaso ya ce alamar na nufin yaki da talauci da kuma ciyar da ilimi gaba.

Rikicin cikin gidan Jam'iyyar NNPP

Tun bayan faduwar jagoran NNPP, Rabi'u Kwankwaso zaben shugabancin kasar nan a shekarar 2023 ne ake ta samun baraka tsakanin 'yan jam'iyyar a Kano da na sauran sassan kasar nan.

Ana da labari cewa a watan Satumba ne jam'iyyar ta kori Kwankwaso bisa zargin cin dunduniyar jam'iyyar da wawure kudin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.