Mataimakin Gwamna Ya Bayyana Muhimmin Dalilin da Ya Sa Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP
- Mataimakin gwamnan jihar Edo, Omobayo Godwins, ya faɗi alkawarin da aka masa wanda ya sa ya sauya sheka daga LP zuwa PDP
- A ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024 aka rantsar da Godwins a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Edo bayan tsige Philip Shaibu
- Da yake hira a wani shirin siyasa a yau, Godwins ya ce rigingimun cikin gida na ɗaya daga cikin manyan dalilinsa na barin jam'iyyar LP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Sabon mataimakin gwamnan jihar Edo, Omobayo Godwins, ya bayyana babban dalilin da ya ja hankalinsa har ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP.
Godwins ya ce ya fice daga Labour Party (LP) zuwa PDP ne saboda jam'iyyar ta masa alƙawarin samun kyakkyawar makoma da ci gaba a siyasance.
Matashin sabon mataimakin gwamnan ɗan kimanin shekara 37 ya faɗi haka ne yayin da ya baƙunci shirin 'Siyasa a Yau' na Channels tv ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Nation ta tattaro cewa Mista Godwins ya karɓi rantsuwar kama aiki a gidan gwamnatin Edo da ke Benin City ranar Litinin, ga watan Afrilu, 2024.
Meyasa Godwins ya koma PDP?
A cewar Godwins, ya bar jam'iyyar LP ne domin goyon bayan dan takarar gwamna na PDP a zaben gwamnan Edo da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba, Asue Ighodalo.
Matashin ya zama mataimakin gwamnan watanni ƙalilan gabanin ƙarewar wa'adin shekaru takwas na Gwamna Godwin Obaseki.
Sai dai ya ce wannan wata alama ce da ke nuna ɗan takarar PDP, Ighodalo, zai lallasa manyan abokan karawarsa, Olumide Akpata na LP da Monday Okpebholo na APC.
Godwins ya jaddada cewa goyon bayan da yake da shi a daga tushensa a Akoko Ado, ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin Edo ta Arewa zai taimakawa Ighodalo a zaɓe.
LP ta canza daga zaɓen 2023
Ya ce jam’iyyar LP ta canja gaba daya daga yadda take a lokacin zabukan 2023 lokacin da ya sha kaye a zaben dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Akoko-Edo.
Ya bayyana rashin jituwa da rarrabuwar kai wanda aka gaza lalubo bakin zaren a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a matsayin wasu dalilansa na barin LP zuwa PDP.
Matashin ya maye gurbin Philip Shaibu, wanda majalisar dokokin jihar Edo ta tsige daga matsayin mataimakin gwamna.
Jam'iyyar PDP na tsaka mai wuya
A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP ta sake shiga sabuwar matsala yayin da ƴan majalisar wakilan tarayya 60 suka yi barazanar ficewa daga cikin jam'iyyar.
Ƴan majalisun sun yi barazanar barin PDP ne matuƙar ba a sauya muƙaddashin shugaban jam'iyyar, Umar Damagum ba.
Asali: Legit.ng