Rikicin El-Rufai da Uba Sani: PDP Ta Gaji da Lamarin, Ta Nemo Mafita Ga Gwamnan Kaduna
- Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna ta shawarci Gwamna Uba Sani da ya kafa kwamitin bincike domin daukar mataki kan Nasir El-Rufai
- Jam’iyyar ta ce hakan ne kadai zai tabbatar da gaskiya kan tulin bashi da kuma karkatar da makudan kudi da aka yi a tsohuwar gwamnatin
- Kakakin jam’iyyar a jihar, Abraham Catoh shi ya bayyana haka a jiya Juma’a 5 ga watan Afrilu inda ya ce suna goyon bayan binciken
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna – Yayin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin Gwamna Uba Sani da Nasir El-Rufai, jam’iyyar PDP ta ba da shawara.
Jam’iyyar reshen jihar ta shawarci Uba Sani da ya binciki tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai kan bashi da lalata jihar.
Wace shawara PDP ta ba Sani kan El-Rufai?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar, Abraham Catoh ya fitar a jiya Juma’a 5 ga watan Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Catoh ya ce jam’iyyar ba ta yi mamakin abin da Gwamna Uba Sani ya fada ba kan gwamnatin Nasir El-Rufai, cewar Arise TV.
PDP ta bukaci gwamnan ya kafa kwamiti mai karfi domin tabbatar da binciken lamarin tare da daukar mataki, cewar TheCable.
PDP ta ce daman ta san haka zai faru
“Ba mu yi mamakin abin da gwamnan ya fada ba, wannan kawai asiri ne ya tonu daga cikin abubuwan da aka yi, muna bukatar a yi bincike domin gano gaskiya.”
“A matsayinmu na jam’iyyar adawa muna goyon bayan kawo ayyukan ci gaba jihar Kaduna, kuma muna Allah wadai da sabanin haka.”
- Abraham Catoh
Yadda Shehu Sani ya ja kunnen El-Rufai
A baya, mun baku labarin cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana irin shawarar da ya ba tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kan bashi.
Sani ya ce ya ja kunnen El-Rufai a wancan lokaci amma mutane suka rika cin mutuncinsa saboda ya fadi gaskiya.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya bayyana tulin bashi da ya gada daga uban gidansa, Nasir El-Rufai.
Asali: Legit.ng