"Da Yiwuwar a Tsige Shi" An Baiwa Mataimakin Gwamna Damar Ƙarshe Kan Zargin da Ake Masa
- Kwamitin bincike ya bai wa mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamred Philip Shaibu dama ta karshe ya bayyana domin kare kansa
- Babban alƙalin jihar Edo ya kafa kwamitin mai mutum bakwai domin bincikar zargin da ake wa Shaibu wanda majalisa ke shirin tsigewa
- Lauyan mataimakin gwamnan ya janye daga halartar zaman kwamitin tun da aka yi watsi da buƙatarsa na jiran hukuncin kotu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Kwamitin mutum bakwai da ke binciken zarge-zargen da ake wa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya ɗaga zamansa zuwa ranar Jumu'a (yau).
Kwamitin ya ɗauki wannan matakin ne domin bai wa Shaibu damar kare kansa daga zarge-zargen, waɗanda majalisar dokokin Edo ke shirin tsige shi a kansu.
A cewar kwamitin, an ɗage zaman ne saboda wanda ake tuhuma watau mataimakin gwamna da lauyansa ba su halarci zaman ba, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka ƙara ba Shaibu dama?
Mai shari'a S.A. Omonua (mai ritaya), shugaban kwamitin ya bayyana cewa kara lokacin zuwa ranar Jumu'a ya zama dole domin bai wa Shaibu damar kare kansa.
Ɓangaren wanda ake zargi ko lauyansa ba su halarci zaman da kwamitin ya yi ranar Alhamis ba, amma ɓangare masu kara sun je wurin.
Mai shari’a Omonua, wanda ya dage zaman, ya nanata bukatar wanda ake tuhuma ya bayyana gaban kwamitin domin ya kare kansa.
“A jiya mun dage zaman zuwa yau (Alhamis) domin wanda ake kara ya zo ya kare kansa. Har yanzu za mu ba wanda ake tuhuma damar zuwa ya kare kansa, to amma kuna gani har yanzu bai zo ba," in ji shi.
Shaibu ya janye daga zuwa zaman
Idan baku manta ba, lauyan Shaibu, Farfesa Oladoyin Awoyale (SAN), ya janye daga halartar zaman ranar Laraba bayan da kwamitin ya yi watsi da bukatarsa.
Awoyale dai ya musanta ci gaba da binciken mataimakin gwamnan saboda babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a dakatar da binciken.
Ya kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne a ranar 28 ga Maris, sannan ta ɗage sauraron karar zuwa ranar 8 ga Afrilu.
Bisa haka ya roƙi kwamitin ya jira hukuncin da babbar kotun tarayya za ta yanke kan lamarin a ranar 8 ga watan Afrilu, 2024, rahoton Guardian.
Gwamnan Ondo ya shirya shiga zaɓe
A wani rahoton kuma kun ji cewa duk da ana ganin abin ba zai zo masa da sauƙi ba, gwamnan jihar Ondo ya nuna fatan samun nasara a zaben fitar da ɗan takara.
Yayin da ake tunkarar zaben gwamna a Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ce yana da ƙwarin guiwa doke ƴan takara 15.
Asali: Legit.ng