Ministan Tinubu Ya Fadi Wahayin da Ya Samu Kan Wa’adin da Shugaban Zai Yi a Mulki
- Dave Umahi, Ministan ayyuka ya ce Shugaba Bola Tinubu ya na kan hanya madaidaiciya a kokarin inganta Najeriya
- Umahi ya ce tabbas ubangiji ya fada masa cewa wannan gwamnati za ta shafe shekaru takwas a kan mulkin kasar
- Ministan ya bayyana haka ne a yau Lahadi 31 ga watan Maris yayin hira da gidan talabijin na Channels a birnin Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Ministan Ayyuka a Najeria, Dave Umahi ya ce ya samu wahayi kan wa’adin da Shugaba Bola Tinubu zai yi a mulki.
Umahi ya ce a rubuce ya ke Tinubu zai shafe shekaru takwas ya na mulkin Najeriya ba tare da wata matsala ba.
Abin da Minista ya da kan wa'adin Tinubu
Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yammacin yau Lahadi 31 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce zuwan Tinubu kan mulkin nan daga ubangiji ne kuma sai ya karisa abin da aka aiko shi da ya yi a Najeriya.
“Dole ku sani cewa Ubangiji ne ya kira Tinubu ya daura masa wannan nauyi, idan ubangiji ya fara abu, zai karisa shi.”
“Ina mai baku tabbacin cewa ubangiji ya fadamin cewa wannan gwamnati za ta shekara takwas akan mulki.”
- Dave Umahi
Ya fadi shirin Tinubu kan 'yan Najeriya
Umahi ya ce Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da kawo sauyi a kasar inda ya ce ya na kan hanya mai kyau a yanzu da irin ayyukan da ya ke yi.
Ya ce ganin yadda Tinubu ke kokarin kawo sauyi kowa ya san ya na aikin ubangiji ne da ya kawo shi kan mulkin kasar.
Remi Tinubu ta fadi shirin Bola
A wani labarin, Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ya fadi yadda Shugaba Bola Tinubu ya himmatu wurin inganta Najeriya.
Remi ta ce shugaban kullum kokarinsa shi ne kawo sauyi a kasar da inganta ta fiye da yadda ya same ta.
Sanata Remi tabayyana haka ne yayin buda baki da matan tsoffin shugabannin Najeriya da kuma matan gwamnoni a Abuja.
Asali: Legit.ng