Tinubu @ 72: Yadda Aka Taya Shugaban Kasa Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Tinubu @ 72: Yadda Aka Taya Shugaban Kasa Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

  • Ranar da aka haifi Mai girma Bola Ahmed Tinubu ta zagayo, a makon nan ya cika shekara 72 da zuwa duniya
  • Fitattun mutane da shugabanni sai aikawa da sakon taya murna suke yi zuwa ga shugaban kasar Najeriyan
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu yabon magabacinsa a mulki zuwa shugaban majalisar dattawa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya cika shekaru 72, manyan ‘yan siyasa da sauran al’umma su na ta kwarara sakon taya shi murna.

Daga cikin wadanda suka aika sakon murna akwai shugaban majalisar dattawa na kasa.

Tinubu @ 72
Shugaba Bola Tinubu ya cika shekara 72 da haihuwa Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Tinubu: Kashim Shettima ya yabi Mai gidansa

Kashim Shettima ya aikawa mai gidansa sakon taya murna a shafin X, ya jinjinawa gwagwarmaya, siyasa da kasuwancinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu @72: Abin da Buhari ya fadawa Bola bayan ya kira shi musamman a waya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga kishin kasa, mataimaki shugaban Najeriyan ya ce Tinubu ya yi fice wajen ganin ya taimakawa wadanda ke kusa da shi.

Akpabio ya ce Tinubu ya cika gwarzo

Godswill Akpabio ya fitar da jawabi na musamman ta bakin Mai taimakawa wajen yada labarai da hulda da jama’a, Eseme Eyiboh.

Premium Times ta ce Godswill Akpabio ya bayyana Mai girma Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban da yake kawo sauyi.

Shugaban majalisar yake cewa tun yana gwamna a Legas, Tinubu ya kawo cigaba, kuma ya iya zakulo kwararrun da za suyi aiki.

"A yayin da ka cika shekara 72 a yau, Ni da iyalina da mutanen mazaba ta a Akwa Ibom da kuma majalisar tarayya, muna yi maka fatan koshin lafiya da shekaru masu albarka nan gaba."

- Godswill Akpabio

APC ta aikawa Shugaba Tinubu sako

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su iya tsige shi daga mulki

Ita kuwa APC ta bayyana Bola Tinubu da hakikanin mai kishin kasa, jagora mai hanken nesa da ya ba damukaradiyya gudumuwa.

Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka ya fitar da jawabi a X a ranar Juma’a domin taya Tinubu murnar cika 72.

Ba a bar shugaban masu rinjaye a majalisa dattawa, Opeyemi Bamidele a baya ba, ya taya tsohon mai gidansa murnar wannan rana.

Sanata Bamidele ya fitar da jawabi da ya yi wa take da “Barka shugaban al’umma.”

Buhari ya kira Tinubu a waya

Muhammadu Buhari ya kira Bola Tinubu a wayar salula, ya jaddada goyon bayansa ga magabacin nasa, ya yi masa fatan alheri.

Garba Shehu wanda shi ne mai magana da yawun tsohon shugaban ya ce a shirye Buhari yake ya ba shugaban kasar goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng