Jam'iyyar Adawa Ta Faɗi Wanda Za Ta Ba Tikitin Takara Domin Ya Kayar da Tinubu a 2027
- Jam'iyyar LP ta fara shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a 2027 bayan ta sha kashi a hannun APC a zaɓen 2023
- A wurin babban taron Labour Party na ƙasa, jam'iyyar ta ba da shawarin sake miƙa tikitin takarar shugaban ƙasa ga Mista Peter Obi
- Haka nan kuma ta kada kuri'ar aminta da jagorancin Gwamna Alex Otti na Abia tare da ware masa tikitin tazarce a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Jam'iyyar adawa Labour Party (LP) ta ba da shawarin tanadar tikitin takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027 ga tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.
Jam'iyyar ta fara shawarwarin sake tsayar da Obi takara ne yayin da ta ke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 mai zuwa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Har ila yau, jam’iyyar LP na son a keɓe tikitin takarar gwamna ga gwamnan jihar Abia, Alex Otti, bisa abin da ta bayyana a matsayin bajintar da ya yi tun da ya shiga ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan babban taron jam’iyyar LP na kasa, wanda aka gudanar a Nnewi, jihar Anambra, ranar Laraba.
LP ta fara shirin tunkarar 2027
Sanarwar ta ce:
"Duba da ƙoƙarin ɗan takarar shugaban kasa a lokacin zaɓen 2023, mun ba da shawarin sake keɓe titikin takarar shugaban ƙasa na LP ga Peter Gregory Obi, jagoran jam'iyya na ƙasa.
"Bugu da kari, taron ya kuma yi nazari kan ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da bajintar gwamnan jihar Abia, mai girma Dakta Alex Otti, tare da kada kuri’ar amincewa da shi.
"Sannan mun ba da shawarar a kebe wa Dakta Alex Otti tikitin takarar gwamnan jihar Abia na babban zaɓen 2027."
Mista Obi, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP a zaɓen 2023, inda ya sha ƙasa a hannun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, rahoton Ripples Nigeria.
Bayan ya samu kuri’u 6,101,533, tsohon gwamnan ya zo na uku a bayan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 6,984,520 kuma ya zo na biyu.
Ƴan majalisa 6 sun fice daga LP
Rahoto ya zo cewa yayin da Labour Party ke fama da rikicin cikin gida, mambobi 6 na majalisar dokokin jihar Enugu sun sauya sheƙa zuwa PDP.
Sun bayyana cewa sun gaji da matsalolin da suka dabaibaye LP a matakin ƙasa da jihohi, bisa haka suka koma PDP domin yi wa al'umma hidima.
Asali: Legit.ng