Jam'iyyar NNPP Ta Samu Sabon Shugaba Na Kasa, Cikakkun Bayanai Sun Fito
- Ajuji Ahmed ya zama sabon shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa
- Jam’iyyar ta sanar da naɗinsa ne a wata sanarwa ranar Talata, 26 ga watan Maris, ta hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Yakubu Shendam
- A cewar kakakin jam’iyyar NNPP, Ahmed ya karɓi ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar ne daga Alhaji Abba Kawu Ali wanda ya yi murabus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a ranar Talata, 26 ga watan Maris, ta sanar da naɗin Ajuji Ahmed a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Ahmed ya karɓi ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar daga hannun Abba Kawu Ali.
Ali ya yi murabus daga muƙaminsa ne a taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC) a ranar Talata, 26 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa shugaban NNPP ya yi murabus?
Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar Yakubu Shendam ya fitar ta ce Ali ya yi murabus ne bisa shawarar likitansa.
Sabon shugaban, Ahmed, shi ne mataimakin sakataren jam’iyyar NNPP na ƙasa kuma babban mai muƙami a jam’iyyar daga yankin Arewa maso Gabas, rahoton gidan talabijin na Channels tv ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Abba Kawu Ali, a yayin taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) a hedkwatar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja, ya ce ya yanke shawarar yin murabus a matsayin shugaban riƙo na ƙasa ne bisa shawarar da likitansa ya ba shi.
"Hakan ne ya sa aka gabatar da ƙudirin naɗin sabon shugaban riko na ƙasa, inda aka amince zaɓen Dakta Ajuji Ahmed."
NNPP na nan daram a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jigon jam’iyyar NNPP a Najeriya, Razaq Adebigbe ya ce jam’iyyar a jihar Kano ta na nan da karfinta.
Razaq ya bayyana haka ne yayin da ake jita-jitar cewa jam’iyyar ta fara samun rauni a jihar saboda wasu matsaloli.
Asali: Legit.ng