Shin Zai Koma APC? Gwamnan PDP Ya Bayyana Dalilin 1 da Ya Sa Ba Zai Yaƙi Shugaba Tinubu Ba

Shin Zai Koma APC? Gwamnan PDP Ya Bayyana Dalilin 1 da Ya Sa Ba Zai Yaƙi Shugaba Tinubu Ba

  • Duk da banbancin jam'iyyun siyasa, gwamnan jihar Akwa Ibom ya ce ba zai yarda ya taƙali faɗa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba
  • Fasto Umo Eno ya gargaɗi mambobin PDP da ɗaruruwan masu sauya sheka zuwa jam'iyyar su guji zagin shugabanni kamar Tinubu
  • Gwamna Eno na PDP ya ce ba zai yiwu mutum ya yaƙi wanda ke ba shi kuɗi ba kuma ya yi tunanin kuɗin nan za su ci gaba da shigowa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa ba zai yarda faɗan siyasa ya shiga tsakaninsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba.

Duk da ba jam'iyyarsu ɗaya ba, Gwamna Eno, mamban jam'iyyar PDP ya gargaɗi mambobin jam'iyyarsa su guji ɗabi'u mara kyau musamnam zagin jagororin siyasa.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa sanatoci a wurin buɗa bakin azumin watan Ramadan a Villa

Bola Tinubu da Gwamna Eno.
Gwamnan Akwa Ibom zai zauna lafiya da Tinubu a siyasance Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Umo Eno
Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne yayin da yake karɓan ɗaruruwan masu sauya sheƙa daga jam'iyyun APC, YPP, ANPP da sauransu zuwa PDP mai mulki a Akwa Ibom.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya gargadi masu sauya shekar da su kaucewa munanan halayen siyasa a cikin jam’iyyar, musamman zagin shugabannin siyasa, Leadership ta ruwaito.

Da yake jawabi ga shugabanni, dattijai, matasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyun adawa a filin taro na Ibom Hall da ke Uyo ranar Juma’a, Gwamna Eno ya bukaci su zama masu hali nagari.

Eno ya roƙe su da su yi aiki tare da gwamnatin jihar tare da kokarin inganta kyakkyawar alakar da ke tsakanin jihar Akwa Ibom da gwamnatin tarayya.

Meyasa Gwamna Eno ya ɗauki wannan matakin?

A kalamansa, Gwamna Eno ya ce:

"Ba zan yi faɗa da shugaban kasa Tinubu ba, ba zai yiwu mu shiga takun saka da cibiyar ƙasa ba. Muna da shugaban ƙaa ɗaya ne kacal a kasarmu kuma ya zama tilas mu guji zaginsa."

Kara karanta wannan

Ramadan: Magidanci ya bayyana yadda yake tafiya mai nisa don samun abincin buda baki ga iyalansa

"Ba zamu yi amfani da kuɗin jihar Akwa Ibom mu yaki asalin cibiya ta ƙasa ba sabida idan muka yaƙe su abun ba zai yi daɗi ba.
"Ba zai yuwu ka yaƙi mutumin da ke tura maka kuɗi ba kuma ka yi tsammanin zai ci gaba da turo maka."

Idan baku manta ba a kwanakin baya, Gwamna Eno ya sha alwashin cewa zai ci gaba da goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

El-Rufai ya gana da Sanata Ningi

A wani rahoton kuma Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya kai ziyara gidan Sanata Abdul Ningi, wanda majalisar dattawa ta dakatar kwanan nan

Majalisa ta dakatar da Sanata Ningi, mamban jam'iyyar PDP mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya saboda zargin cushe a kasafin kuɗin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262