Bola Tinubu Ya Bayyana Ɗan Takarar da Zai Lashe Zaben Gwamnan Jihar Edo a 2024
- Bola Ahmed Tinubu ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC za ta lashe zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa a watan Satumba, 2024
- Shugaban ƙasa ya kuma miƙa tutar APC ga ɗan takarar gwamna, Sanata Monday Okpebholo, da abokin gaminsa, Honorabul Dennis Idahosa
- Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ja hankalin mambobin APC cewa akwai bukatar haɗin kai a cikin gida domin samun nasara a zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya ce All Progressives Congress (APC) ta kama hanyar samun nasara a zaben gwamnan jihar Edo da za a yi a watan Satumba, 2024.
Tinubu ya nuna kwarin guiwar cewa ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Sanata Monday Okpebholo, ne zai lashe zaɓen yayin da yake miƙa masa tutar jam'iyya a Aso Villa.
Shugaban ƙasar ya mika wa ɗan takarar tutar jam'iyyar APC tare da ɗan takarar mataimakin gwamna, Dennis Idahosa, a fadar shugaban kasa ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC: "Za mu goya masu baya" - Tinubu
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa yayin da yake jawabi ga ƙusoshin APC karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Tinubu ya ce zasu marawa ƴan takarar baya.
"Idan kuna farin ciki, muna muna farin ciki, idan kun shirya mu ma a shirye mu ke, za mu tsaya tsayin daka a bayanku kamar bangon Gibraltar.
"Wannan ne kaɗai abin da zan gaya muku, jam'iyyarmu tana da girma amma nasara tana matsayi mafi grma kuma tana da matuƙar muhimmanci.
- Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu ya yabawa shugabannin jam’iyyar na jihar Edo bisa aiki tuƙuru da kokarin da suka yi har ƴan takarar suka samu nasara.
Ya kuma yabawa Sanata Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar bisa kyakkyawan jagorancin da yake yi wanda ya zama abin koyi.
Ganduje ya buƙaci a haɗa kai wuri guda
Tun da farko a jawabinsa, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya jaddada bukatar hadin kan jam’iyyar a cikin gida domin samun nasara a zaben.
A rahoton The Nation, Ganduje ya ce:
"Ɗan takararmu yana da taushin magana. yana da maida hankali kuma mai jinin nasara ne. Ina da yaƙinin kasancewarsa ɗan takarar mu, zamu kwato jihar Edo ta dawo hannun APC."
Ramadan: Uba Sani ya kaddamar da raba tallafi
A wani rahoton na daban kuma Gwamnan Kaduna ya kaddamar da fara rabon kayan tallafi karo na biyu ga mazauna jihar domin cika umarnin shugaban ƙasa.
Malam Uba Sani ya ce a wannna karon gwamnati za ta raba tireloli 128 na shinkafa da masara ga talakawa, gajiyayyu da marasa galihu.
Asali: Legit.ng