Kujerar Shugaban Jam'iyyar Adawa Ta Shiga Tangal-Tangal, Bayanai Sun Fito

Kujerar Shugaban Jam'iyyar Adawa Ta Shiga Tangal-Tangal, Bayanai Sun Fito

  • An taso shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, Julius Abure, da ya yi murabus daga muƙaminsa
  • Ɓangaren siyasa na ƙungiyar NLC, ya zargi Abure da laifin yin kaka-gida wajen gudanar da lamuran jam'iyyar
  • Ta kuma soki matakin da ya ɗauki na shirya babbar taron jam'iyyar na ƙasa a ɓoye inda ta ce hakan ya saɓa doka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Kwadago ta ƙasa (NLC) ta soki salon shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) ta ƙasa Mista Julius Abure.

NLC ta kuma buƙaci Abure da ya yi murabus nan take a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa, cewar rahoton jaridar The Nation.

An bukaci Abure ya yi murabus
An bukaci Julius Abure ya yi murabus daga shugabancin Labour Party Hoto: Barrister Julius Abure, Labour Party
Asali: Facebook

Ta kuma buƙaci da ya kafa da kwamitin riƙon ƙwarya domin shirya babban taron jam’iyyar na ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake son Abure ya yi murabus?

NLC ta ci gaba da cewa, neman yin murabus ɗin da ta buƙaci Abure ya yi, ta yi ne domin ceto jam'iyyar daga halin da ya jefata.

Ta zargi Abure da tafiyar da jam'iyyar shi kaɗai da yin kaka-gida a kan lamuran jam'iyyar.

Ƙungiyar ta kuma bayyana sanarwar da Abure ya yi na babban taron jam’iyyar Labour na ƙasa a matsayin wanda ya saɓawa doka, inda ta ƙara da cewa ba za ta lamunci a riƙa yi wa doka karan tsaye ba wajen gudanar da harkokin jam’iyyar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ɓangaren siyasa na NLC, Titus Amba da sakatarensa Chris Uyot suka rattaɓawa hannu, rahoton jaridar Nigerian Tribune ya tabbatar.

Abure dai yana takun saka da wasu jiga-jigan jam'iyyar kan yadda yake tafiyar da jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi kudin fansan da gwamnatinsa za ta biya don ceto daliban da aka sace a Kaduna

A watan da ya gabata ne ma’ajin jam’iyyar ta ƙasa Oluchi Opara ta zargi Abure da karkatar da naira biliyan 3.5 na kudaden da jam’iyyar ta siyar da fom din tsayawa takara da kuma gudummawar da aka samu don yaƙin neman zaɓen 2023.

An buƙaci soke rajistar LP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya ta kai ƙarar jam'iyyar adawa ta Labour Party (LP), ƙara a gaban kotun babbar tarayya da ke Abuja.

Ƙungiyar na neman kotun da ta soke rajistar jam'iyyar saboda ta keta kundin tsatin mulkin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng