Shugaba Tinubu Ya Jero Mutanen da Suka Koma Yaƙarsa Saboda Matakan da Ya Ɗauka a Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu ya ce masu amfana da tallafin man fetur a ƴan fasa kwauri ba su haƙura ba, sun koma suna yaƙar gwamnati
- Yayin ganawa da shugabannin APC na jihohi, Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana domin inganta rayuwar jama'a
- Shugaban kasar ya ce ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen kare dukiyar talakawa, yana mai cewa akwai masu yin zagon kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ƴan fasa kwauri da masu cin gajiyar tallafin man fetur sun fara yaƙarsa sabida matakan da ya ɗauka.
Amma duk da haka shugaban kasar ya lashi takobin cewa gwamnatinsa ba zata ci amanar da ƴan Najeriya suka ɗora masa ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya
Tinubu ya yi wannan furucin ne a wurin ganawarsa da shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihohi a Aso Villa da ke Abuja ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Najeriya za ta yi galaba kan duk wasu masu shirin kawo hargitsi da kuma waɗanda ake zargin suna yin zagon kasa ga kokarin sake fasalin tattalin arzikin kasa.
A wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kara da cewa gwamnatinsa ta tura karin kayan aiki ga ɓangarori masu muhimmanci a rayuwar ƴan Najeriya.
Yaushe za a kawo ƙarshen wahala a Najeriya?
A ruwayar Channels tv, Tinubu ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana domin inganta rayuwarsu da jin daɗi da walwala.
“Yayin da muke yaki da cin hanci da rashawa, masu fasa-kwauri da tsofaffin masu cin gajiyar tallafin man fetur, tabbas za su dawo suna yaƙar mu.
"Amma za mu yi kokarin kare mutanenmu. Dukiyar baitul-mali ta jama'a ce, kuma ba za mu bari a ci amana ba.
“Na kafa kwamiti mai ƙunshe da gwamnoni, kuma mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne zai jagorance su. Za su yi aiki ne domin lalubo abin da ya kamata a yi domin inganta rayuwar al'umma."
- Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu ya ɗauko kwamishinan PDP
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya ɗauke kwamishinan ayyukan jihar Ribas bayan ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar BCDA.
Dakta George-Kelly Alabo ya yi murabus daga mukamin kwamishinan ayyuka a gwamnatin Fubara saboda naɗin da Tinubu ya masa.
Asali: Legit.ng