"Har Yanzu Ni Mamban Jam'iyyar PDP Ne" Ministan Tinubu Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

"Har Yanzu Ni Mamban Jam'iyyar PDP Ne" Ministan Tinubu Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙara jaddada cewa har yanzu shi mamban jam'iyyar PDP ne duk da ƙoƙarin wasu jiga-jigai na ganin an kore shi
  • Tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana haka ne yayin hira da wasu zaɓaɓɓun yan jarida a Abuja, ya ce babu abin da ya canza
  • Wike dai ya samu saɓani da manyan PDP a lokacin da ake shirin tunkarar zaben shugaban kasa na 2023, ya goyi bayan Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Mista Nyesom Wike, ya ce har yanzu shi mamba ne a babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, ministan ya yi wannan furucin ne yayin da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP ke masa barazanar kora daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Cushe a kasafin 2024: PDP ta bukaci Akpabio ya yi murabus, an samu karin bayani

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Har Yanzu Ni Mamban Jam'iyyar PDP Ne, Ministan Abuja Wike Hoto: Mr. Nyesom Wike
Asali: Facebook

Rikicin Nyesom Wike a jam'iyyar PDP

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas, ya samu saɓani da shugabannin jam'iyyar PDP a daidai lokacin da ake tunkarar zaben shugaban kasa na 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya dage cewa ya zama tilas jam’iyyar ta ci gaba da bin tsarin raba madafun iko a cikin gida ta hanyar miƙa tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya.

Bisa haka ne ya ki goyon bayan Atiku Abubakar daga Arewacin Najeriya, wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP baya ya doke shi.

Tsohon gwamnan ya koma ya marawa jam'iyar APC mai mulki baya, kuma Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar zama shugaban ƙasa a bara.

Wike na nan a PDP ko ya koma APC?

Daga baya Tinubu ya nada shi minista, lamarin da ya janyo cece-kuce kan ko har yanzu Wike na cikin jam’iyyar PDP ko kuwa ya koma APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon shugaban PDP da wasu mutum 2 a manyan muƙamai

Ministan babban birnin tarayya Abuja ya ce har yanzu shi 'dan jam’iyyar PDP ne, inda ya tabbatar da nunka goyon bayansa ga Shugaba Tinubu, Sahara Reporters ta rahoto.

"Ni mamban jam’iyyar PDP ne,” in ji shi yayin wani taron manema labarai da zababbun ‘yan jarida a Abuja,
"kun taba ganin na canza wani abu?"
“Ina nan daram a PDP ban boye ba: na ce musu ba zan goyi bayan dan takararsu na shugaban kasa ba.
Shin saboda na yi magana ne ko kuma na yi abin da mutane ba su fahimta ba?"

- Nyesom Wike.

Tinubu ya ƙara naɗa darakta a CBN

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya naɗa wanda zai maye gurbin Mista Kalu Eke, wanda ya ƙi karɓan tayin muƙami a babban bankin Najeriya (CBN)

Shugaba Tinubu ya roki majalisar dattawa ta amince da naɗin Dakta Ruby Onwudiwe a matsayin mamban majalisar daraktocin CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262