Abdul Ningi: Shehu Sani Ya Lissafo Matsalolin da Sanatan Zai Fuskanta, Ya Fadi Mai Cetonshi
- Sanata Shehu Sani ya magantu kan dakatar da Sanata Abdul Ningi da aka yi a Majalisar inda ya fadi abubuwan da zai fuskanta
- Tsohon sanatan ya ce shi ma ya taba fuskantar irin wannan matsala inda ya ce shugaban Majalisar a wancan lokaci shi ya cece shi
Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na X kan lamarin dakatar da Sanata Ningi da Majalisar ta yi game da wasu zargi masu nauyi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Sanata Shehu Sani ya yi magana bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa a jiya Talata 12 ga watan Maris.
Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya ya ce ya fuskanci irin wannan matsalar inda ya ce shugaban Majalisar a wancan lokaci, Bukola Saraki ne ya cece shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya kawo labarinsa a majalisa
Sanatan ya ce babban laifin da ya aikata a idon Majalisar shi ne ya bukaci sanatocin su bayyana albashin da suke dauka ga al’umma.
Ya lissafa abubuwa hudu da Sanata Ningi zai fuskanta saboda dakatar da shi da aka yi a Majalisar tarayya wanda su na da tsauri.
“Dakatarwa a Majalisa na nufin Sanatan ba zai halarci zaman Majalisar ba da kuma duk wani taro na kwamitin da ya ke ciki.”
“Sanatan ba zai samu albashi da duk wasu hakkoki ba kuma ba zai samu damar shiga ofis ko zuwa kusa da harabar Majalisar ba har sai kwanakin sun kare.”
- Shehu Sani
Dalilin dakatar da Sanata Abdul Ningi
Wannan na zuwa ne bayan Majalisar ta dakatar da Sanata Ningi bayan zargin da ya yi cushe a cikin kasafin kudin shekarar 2024.
Ningi ya bayyana irin illar da aka yi wa Najeriya kan karin da aka yi a cikin kasafin kudin na wannan shekara.
Wannan zargin na Ningi ya ta da kura a Majalisar inda wasu ke kiran a hukunta shi bisa wannan zargin karya da ya yi.
An samu hargitsi a Majalisa
A baya, mun ruwaito muku cewa Majalisar Dattawa ta shiga rudani kan wasu zarge-zarge da wani sanata ya yi.
Sanata Jarigbe Jarigbe daga jihar Cross River ya birkita Majalisar inda ya ce an nuna wariya wurin rabon kudi ga manyan sanatoci a Majalisar.
Asali: Legit.ng