Sanata Ningi Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa, Ya Ambaci Dalili
- Sanata Abdul Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ya haƙura da shugabancin ƙungiyar Sanatocin Arewa
- Sanatan wanda majalisar ta dakatar bisa zargin da ya yi na cewa an yi cushe a kasafin kuɗin 2024 ya bayyana murabus ɗinsa ne a cikin wata sanarwa
- Dakataccen sanatan ya ce ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan abubuwan da ke faruwa a majalisar tarayya, yankin Arewa da ƙasar nan baki ɗaƴa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Dakataccen Sanata Abdul Ahmed Ningi ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa na shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.
Hakan na zuwa ne dai bayan dakatarwar da aka yi masa daga zauren majalisar dattawan a ranar Talata, 12 ga watan Maris 2024.
Meyasa Abdul Ningi ya yi murabus?
Sanatan wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya ya ce ya yanke wannan shawarar ne saboda abubuwan da ke faruwa a majalisar tarayya, yankin Arewa da kuma Najeriya baki ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan sai ya gode wa Sanatocin Arewa da suka ba shi damar jagorantarsu a matsayin shugaban ƙungiyar na ɗan ƙaramin lokaci.
Takardar murabus ɗin Sanatan tana ɗauke da kwanan watan ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2024.
Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ne ya sanya takardar a shafinsa na X jim kaɗan bayan dakatar da Sanata Ningi a ranar Talata, 12 ga watan Maris 2024.
Dalilin da dakatar da Sanata Ningi
An dakatar da Sanata Ningi ne bayan ya yi zargin cewa an yi cushen N3.7tr a cikin kasafin kuɗin bana na shekarar 2024.
Wani ɓangare na takardar na cewa:
"Zan yi murabus daga muƙamina na shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa.
"Hakan ya zama tilas ne biyo bayan abubuwan da ke faruwa a majalisar tarayya, yankin Arewa da kuma ƙasa baki ɗaya."
Duba takardar murabus ɗinsa a nan ƙasa:
Ningi ya yi yunƙurin juyin mulki
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Bamidele Opeyemi ya zargi Sanata Ningi da yunƙurin yin juyin mulki na farar hula.
Bamidele ya yi zargin cewa Ningi ya so ya tunzura Sanatocin Arewa ne domin a karɓe mulkin majalisar daga hannun Sanata Godswill Akpabio.
Asali: Legit.ng